Zolaya: APC na jiran saƙon taya murnar cin zaben Ondo daga PDP - Buni

Zolaya: APC na jiran saƙon taya murnar cin zaben Ondo daga PDP - Buni

- Shugaba rikon kwarya na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce jam'iyyarsu na jiran sakon taya murna daga jam'iyyun siyasa kan nasarar zaben Ondo

- Buni ya ce kamar yadda suka taya PDP murna a yayin da ta yi nasarar zaben Edo, ya kamata a rama wa kura aniyarta

- Sai dai babbar jam'iyyar adawa ta bayyana ikirarin Buni a matsayin rashin azanci

Jam’iyyar All Progressives Congress ta ce har yanzu tana zuba idon samun sakon taya murna daga jam’iyyun siyasa musamman daga wajen PDP, a nasarar da ta yi a zaben ranar Asabar na Gwamnan jihar Ondo.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni, ne ya fadi hakan a wata hira da manema labarai a sakatariyar Jam’iyyar na kasa, a Abuja, a ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Zanga-zangar neman a dawo da rundunar SARS na gudana a Borno

Zolaya: APC na jiran saƙon taya murnar cin zaben Ondo daga PDP - Buni
Zolaya: APC na jiran saƙon taya murnar cin zaben Ondo daga PDP - Buni Hoto: @MalaBuni
Asali: Twitter

Buni ya ce: “masu iya magana sun ce, yana da kyau mayar da alkhairi da alkhairi, kuma kamar yadda muka taya PDP murna a zaben Edo, muna jiran ganin sakon taya murna daga PDP da sauran jam’iyyun siyasa.

“Ta hakan, za mu karfafa zabe a Najeriya, maimakon mayar da zabe abun a mutu ko ayi rai.”

Amma da yake martani, babban sakataren PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana tsammanin Buni a matsayin rashin tunani.

Ologbondiyan ya ce: “abun dariya ne cewa Gwamna Buni na barar samun yardarmu kan zaben duk da yana sane da cewar akwai tangarda a tsarin da ya kai dan takarar jam’iyyarsa ga nasara."

KU KARANTA KUMA: Ruguza rundunar SARS: Ka buɗe idanuwanka da kyau - Shawarar Marafa ga Buhari

"Maimakon rokar sakon taya murna daga PDP, kamata yayi ace Buni ya yi magana kan satar kudin da ake yi don daukar nauyin jam’iyyarsa ta hanyar siyan kuri’u a hannun yan Najeriya da ke fama da radadin karin farashin man fetur, da kuma rashawa da ake a fannin mai karkashin APC.”

A wani labari, Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi hadimarsa ta Soshiyal Midiya, Lauretta Onochie, a matsayin daya daga cikin kwamishanonin hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC.

Buhari ya gabatar da sunanta da wasu mutane uku gaban majalisar dattawa domin tantancesu da tabbatar da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng