Kalli abun mamaki wani manomi ya kera inji bambaran masara

Kalli abun mamaki wani manomi ya kera inji bambaran masara

Bayan kunga hotunan abun da wannan manomin yayi, zaku gane cewar mutum ya fuskanci wata jarabta a rayuwa ma wani abune na karin hikima.

Kalli abun mamaki wani manomi ya kera inji bambaran masara

Manomin kenan alokacin da yake bambaran masaransa daya noma da injin daya hada na bambare masara da kansa

Duk yawancin mutane da suke kirkiro abu da kansu a wurare, yawancin su matsine kesa suyi tunanin kirkiro su. Domin su biyama kansu bukatar data damesu alokacin. Saboda da haka anan muna iya cewar dole takansa mutane su dinga kirkiran wasu na'urori da kansu domin kuwa ba kowa bane yake iya siyo na'ura daga kasar waje domin bukatar kansa.

Saboda haka mutane suke kokarin bullo da wasu sabbin hikimomi wajen yin na'urorin gargajiya domin ragema kansu wahalhalun wasu aiyuka. Haka anan wani manomi yayi kokarin kirkiro da wani inji wanda ke bambare masara.

Kalli abun mamaki wani manomi ya kera inji bambaran masara

Mutumin yana aikin bambaran masara tare da injin daya hada

Mutumin dai yayi kokarin kirkiro da wannan injin ne domin samar ma kansa saukin aikin bambaran masaran, domin kuwa idan yace zaiyi amfani da yadda akeyi a gargajiyence nayin amfani da hannuwan sa to kafin ya bambare masaran da zata cika bokiti to babu shakka zaisha wahala. Saboda haka yayi wannan hikimar tayin amfani da bin hanya mafi sauki tayin amfani da injin daya hada na gargajiya.

Kalli abun mamaki wani manomi ya kera inji bambaran masara

Mutumin yana sanya masara a injin daya keta domin aikin bambara

Wannan manomin ya hada injin bambaran masara wanda zaiyi masa aikin bambaran cikin ruwan sanyi batare da yasha wata bakar wuyaba a aikin bambaran masaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng