Buhari: DEDA ta na so Gwamnatin Tarayya ta fara yasan Kogin Benuwai

Buhari: DEDA ta na so Gwamnatin Tarayya ta fara yasan Kogin Benuwai

- Kungiyar ‘Yan Daura su na so a fara aikin yashe Kogin jihar Benuwai

- DEDA ta ce yin hakan zai taimakawa sauran wasu jihohin da ke Arewa

- Tun 2014 aka ce za ayi aikin, amma har yau ba a iya fara kwangilar ba

An fito an yi kira ga gwamnatin tarayya ta duba rokon da gwamnan jihar Benuwai, Mista Samuel Ortom ya fito ya yi kwanakin baya.

Mai girma Samuel Ortom ya nemi alfarmar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yashe wasu gabobi a kogin Benuwai.

Kungiyar DEDA da aka kafa domin cigaban kasar Daura, ta yi kira da babban murya ga shugaban kasa da ya duba wannan roko.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Daura ya ce zai sa a ba wani kashi saboda suka a Facebook

Shugaban wannan kungiya ta DEDA da kuma takwaransa na kungiyar ainihin mutanen garuruwan Daura da Katsina su ka yi wannan kira.

Alhaji Aliyu Daura ya kai kukansu ne ta hannun jaridar Daily Trust kamar yadda aka fitar da rahoto a jiya ranar 24 ga watan Satumba, 2020.

A cewar Aliyu Daura, akwai bukatar a duba wannan kwangila da aka fara badawa tun shekarar 2014, amma har yau an gaza soma aikin.

Buhari: DEDA ta na so Gwamnatin Tarayya ta fara yasan Kogin Benuwai
Buhari a Daura Hoto: The Nigerian Voice
Asali: UGC

Shugaban wannan kungiya ya ce gwamnatin tarayya ta bada kwangilar ne a kan Naira biliyan 25.9.

KU KARANTA: Edo 2020: Ban kai kasa ba inji Oshiomhole

“Idan an kammala aikin nan, zai bunkasa harkar noma, sannan ya sawake zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa wasu bangarorin Arewacn kasar nan.”

Daura a madadin kungiyarsu, ya bayyana cewa yashe wannan kogi zai sa a rika bin gabar Lokoja zuwa Makurdi a cikin wannan lokaci a shekara.

Don haka ne kungiyar ta roki shugaban kasa da kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya sake kai ido wajen aikin, ya fitar da kudi domin a fara.

A jiya kuma aka ji cewa wasu 'Yan majalisar kasar Ingila sun aikawa kungiyar Common Wealth takarda, ta ce Gwamnatin Tarayya ta gaza.

Takardar ta sanar da kungiyar game da kashe-kashen da ake fama da shi a Arewacin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel