Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rai 1, sun sace mutum 10 a Nasarawa

Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rai 1, sun sace mutum 10 a Nasarawa

- Wasu 'yan bindiga masu tarin yawa sun kutsa garin Kana da ke karamar hukumar Nasarawa

- 'Yan bindigan sun kashe mutum daya tare da sace wasu mutane goma da kuma raunata wasu masu yawa

- Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Mohammed Ottos ya tabbatar da aukuwar lamarin

'Yan bindiga da suka kai 20 a ranar Litinin da dare sun shiga kauyen Kana da ke karamar hukumar Nasarawa. Sun kashe mutum daya tare da sace wasu 10 da kuma barin wasu dauke da raunika.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin daga bakin shugaban karamar hukumar Nasarawa, Mohammed Sani Ottos, ya ce 'yan bindigar sun shiga garin da dare, jaridar Vanguard ta wallafa.

Mohammed Ottos ya ce 'yan bindiga sun shiga garin daga tsaunin Kana, kuma sun koma ta wannan hanyar wacce ta bi ta Kana zuwa Maraba Udege, Onda, Agwada, Nasarawa Eggon zuwa birnin Wamba.

Kamar yadda shugaban karamar hukumar yace, "An tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun fada garin Kana a ranar Litinin inda suka dinga harbi suna tsorata jama'a."

"Na kushe wannan lamarin kuma na ziyarci garin inda na jajanta wa iyalan wanda aka kashe. Na yi jinjina ga kwamandan bataliya ta 177 da ke Keffi wadanda suka raka ni domin jaddada wa mazauna yankin cewa za su basu tsaro," yace.

Wani ganau ba jiyau ba ya yi ikirarin cewa wata mata mai juna biyu da yaro karami, suna daga cikin mutum 10 da aka sace.

KU KARANTA: Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rai 1, sun sace mutum 10 a Nasarawa
Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rai 1, sun sace mutum 10 a Nasarawa. Hoto daga Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA: Budurwar da mahaifiyarta za ta mutu ta shirya aurenta cikin kwana 5, an daura aurenta a cikin asibiti

A wani labari na daban, 'yan uwan wani mutum mai shekaru 37 wanda aka gano ya rasu a hannun 'yan sanda da ke da ofishi a sabuwar Nyanya, Nasarawa, sun zargin 'yan sanda da azabtar da shi har ya mutu.

Donald Agbenge, wanda aka yi wa ganin karshe a wurin aikinsa a ranar 6 ga watan Satumba a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, an ga gawarsa a asibitin sabuwar Karu, inda 'yan sanda suka kai gawarsa a sa'o'in farko na ranar Litinin, 7 ga watan Satumba.

Babban yayan mamacin mai suna Iornumber Agbenge, wanda ya zanta da Aso Chronicle, ya ce sai da ya suma lokacin da 'yan sandan suka sanar masa da cewa kaninsa ya mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel