Yanzu-yanzu: Obaseki da mataimakinsa sun karbi shahadar nasara a zabe

Yanzu-yanzu: Obaseki da mataimakinsa sun karbi shahadar nasara a zabe

- Hukumar zabe ta kammala aikinta na zaben gwamnan jihar Edo

- Aikin karshen bayan sanar da sakamakon zaben shine baiwa wadanda sukayi nasara shahada

- Gwamna Obaseki na jam'iyyar PDP ya doke Ize-Iyamu na APC a zaben gwamnna jihar Edo

Hukumar gudanar da zaben kasa watau INEC ta bada shahadar nasara a zabe ga gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da mataimakinsa, Philip Shaibu, a matsayin wadanda sukayi nasara a zaben ranar Asabar, AIT ta ruwaito.

Da wannan shahadar, Obaseki da Shaibu sun cika sharrudan dokar zabe domin rantsar da su ranar 12 ga Nuwamba, 2020 a Benin City domin wa'adinsu na biyu a ofis.

Yanzu-yanzu: Obaseki da mataimakin sun karbi shahadar nasara a zabe
Yanzu-yanzu: Obaseki da mataimakin sun karbi shahadar nasara a zabe
Source: Facebook

KU KARANTA: Gwamna Babagana Umara Zulum ya nada sabon Sarkin Biu

A ranar asabar, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta tabbatar da Mista Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Edo a karo na biyu bayan ya yi nasarar doke abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC.

Wannan shine karo na biyu da Obaseki ke yin nasara a kan Ize-Iyamu, inda a shekarar 2016 ma hakan ta kasance sai dai a lokacin Obaseki ya yi takara a karkashin APC yayin da Ize-Iyamu ke PDP.

INEC ta sanar da cewa Obaseki ya zama zakara ne a zaben gwamnan bayan samun kuri'u mafi rinjaye na 307,955 inda mai biye masa Ize-Iyamu ya samu kuri'u 223,619.

Wanda ya zo na uku a zaben shine dan takarar jam'iyyar SDP da kuri'u 323, sai na hudu dan takatar jam'iyyar LP da ya samu kuri'u 267.

Hukumar zaben ta ce adadin masu zabe da aka tantance domin kada kuri'a a jihar 557,443, yayin da adadin kuri'u masu sahihanci 537,407.

Jimillar kuri'un da masu zabe suka kada 550,242, sannan kuri'un da suka lalace kuma 12,835.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel