Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan

Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan

- Hira tsakanin mahaifi da diyarsa ya janyo mutuwar auren shekaru 14

- Karamar yarinya ta fallasa boyayyen sirrin mahaifiyar ta ga mahaifinta

- Baya ga taba jikina da sumbata ta babu abinda makwabcinmu yayi cewar matar

Hira ta barke tsakanin wani mahaifi da karamar diyarsa wanda ya jawo asirin matarsa ya tonu har ta kai ga sanadiyyar mutuwar aurensu na shekara 14.

Bayan Steven ya dawo gida sai hira ta barke tsakaninsa da diyarsa har ya tsinci wata magana daga cikin hirarsu.

Yarinyar ta sanar da mahaifinta cewa mahaifiyarta ta shiga gidan makwabta. Mutumin ya cigaba da yiwa diyar tasa tambayoyi, har tace ma sa a lokacin da ta dawo gida ta fara neman mahaifiyar ta ta, sai makwabcinsu ya leko da kansa yace mata yanzu mahaifiyarta zata iso gareta.

Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan
Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan
Source: Facebook

Hakan ya jawo rikici tsakanin ma'auratan kwana daya bayan samun labarin, inda Steven ke tambayar matarsa dalilin shiga makwabta kamar yadda Jaridar Kidsport ta ruwaito.

Da farko ta amsawa mijin nata sama-sama, sai dai sakamakon dadewar mata da mijin tare, mijin yace ya san yadda takeyi idan tayi karya.

KU KARANTA: Diyar Osinbajo ta haihu, ya samu jikansa na farko a duniya

Daga baya ta fito fili tana neman afuwar mijin nata ta sanar masa da cewa a gaskiya sun taba jikin juna kuma sun sumbaci juna wanda tasan hakan da sukayi bai dace ba.

Steven yace: "Nasan yadda take yiwa mutane karya. Kuma na tabbatar ba sumbata kadai su ka tsaya ba."

Ya ce ya fatattaketa daga gidansa amma bayan yaji nasihar mutane sai ya amince ya dawo da ita saboda yaransu.

Steven yace gaskiya wannan al'amari ya shafi tarayyarmu matuka.

Ya kara da cewa: "Gaskiya na rikice gaba daya saboda ina kaunarta sai dai kaunar ta zama tamkar abota amma ba wai soyayyar miji da mata ba."

Mutumin ya nema shawarar mutane akan al'amarin.

Daya daga cikin masu bashi shawara yace: "Ina tunanin a wannan gabar ya kamata kayi nazari mai kyau, duk da taci amanarka ka ga idan zaka iya yafe mata."

Wani kuma yace "Ka nemo abinda zai sa ka manta da wannan lamarin yadda bazai shafi zuri'arku ba, duk da nasan zai dauki lokaci."

KU KARANTA: Bayan ya yiwa saurayin kanwarsa dukan tsiya, saurayin ya siyo mata sabuwar mota mai tsadar gaske a matsayin godiya

A wani bangaren kuwa Legit.ng ta kawo muku yadda aka kama wani babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a cikin ofis a lokacin da rashin sani ya sanya ya fara kiran waya na bidiyo da abokanan aikin shi a kasar Philippines.

Kamar yadda rahoto ya nuna, ma'aikata daga garin Fatima Dos dake Cavite suna gabatar da taro ta manhajar zoom kamar yadda suka saba a ranar Laraba.

Shugabansu Jesus Estil, wanda aka bayyana cewa bashi da ilimi akan harkokin na'ura mai kwakwalwa yaje ya danna wani wuri sai kyamarar na'urarshi ta fara aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel