Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta

Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta

- An samu nasarar ceto rayuwar wata budurwa da ta fado daga saman bene mai hawa takwas

- Budurwar ta fado daga benen ne a yayin da take gujewa saurayinta wanda ya jima yana cin zalinta

- Ta kwashe kwanaki 21 tana kwance a asibiti abinci ma sai ta cikin wani bututu ake bata

Wata budurwa mai suna Georgia Brodick, mai shekaru 22 da ta kware wajen rawa, cikin ikon Allah ta cigaba da rayuwa bayan ta diro daga bene mai hawa takwas a lokacin da take kokarin tserewa saurayinta da yake cin zarafinta.

A rahoton da Daily Mail Australia, ya fitar, Brodrick ta kira mahaifinta da safiyar ranar 17 ga watan Yuli, daga gidanta dake Melbourne, babban birnin kasar Australia, inda ta dinga rokon shi akan yaje ya dauke ta.

Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta
Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta
Source: Facebook

Georgia dai ta gano cewa saurayinta yaci amanarta, bayan dukanta da ya dinga yi a lokuta da dama a baya.

A lokacin da take jiran mahaifinta bai karaso ba, sai ta yi tsalle ta fado daga benen.

Anyi gaggawar garzayawa da ita zuwa asibiti, inda aka ayi gaggawar ceto rayuwarta.

KU KARANTA: Saurayi ya tura wa budurwa N50,000 saboda damar hira da ita da ta bashi a kafar sada zumunta

Ciwon da taji yayi muni sosai, domin kuwa hatta likitocin asibitin sun bayyana cewa zai yi wuya ta rayu, yayin da ta shafe makonni uku tana kwance ana bata abinci daga cikin wani bututu.

Cikin ikon Allah ta rayu, duk da dai ta manta yadda aka yi ta fado daga benen, tana tare da iyayenta a lokacin da ta farfado.

Bayan ta farfado ne take bayar da labarin irin wahalar da ta sha a wajen tsohon saurayinta.

KU KARANTA: Hotuna: EFCC ta damke malaman jami'a 2 da wasu 28 a kan damfara

"Idan nayi kokarin barin gidan da yake, sai ya zauna a gaban kofar gidan ya hanani fita daga gidan," ta ce.

"Iyayena sun yi mini gargadi a kanshi, saboda sun kasa ganin laifin shi, hakan ya sanya ya dinga yi musu karya yana dora musu laifi a kaina.

"Ya sanya naji a raina shine mutum daya a duniya da yake sona fiye da kowa."

Shi kuwa wani matashi mai shekaru 30 ya shiga hannun jami'an tsaro a hammanskraal, yankin arewacin Pretoria sakamakon zarginsa da ake da soka wa tsohuwar budurwarsa wuka har ta mutu.

Matashin ya kashe tsohuwar budurwarsa har lahira bayan ta yi sabon saurayi, kamar yadda jami'an 'yan sandan yankin Guateng suka sanar a ranar Lahadi 13 ga watan Satumban 2020.

Matashiyar mai shekaru 23 ta matukar shan wahala sakamakon sossoka mata wuka da tsohon saurayinta yayi bayan kwashe dongon lokacin da yayi yana sanar da jama'a cewa sai ya kasheta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel