Jama'a masu tarin yawa sun yi wa Sarkin Kano maraba a Ilorin (Hotuna)

Jama'a masu tarin yawa sun yi wa Sarkin Kano maraba a Ilorin (Hotuna)

Cincirindon jama'a sun cika filin sauka da tashin jiragen sama na Ilorin a ranar Alhamis domin yi wa Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, marabar zuwa garin mai tarihi.

Wasu daga cikin jiga-jigan 'yan fadar mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, da fitattun 'yan jihar sun hallara a fadar don yi wa sarkin barka da isowa.

Sarkin Kano ya sauka daga jirgin tare da wasu masu sarautar gargajiya wurin karfe 1:45 na ranar yau Alhamis.

Barka da zuwan da jama'a ke yi masa ne ya ziyarcesa har zuwa lokacin da ya sauka daga jirgin saman.

Jama'a masu tarin yawa sun yi wa Sarkin Kano maraba a Ilorin (Hotuna)
Jama'a masu tarin yawa sun yi wa Sarkin Kano maraba a Ilorin (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Masu rawa da kide-kiden gargajiya sun hallara a filin sauka da tashin jiragen saman domin tarbar basaraken.

Masu achaba dauke da fasinjoji masu son ganin sarkin duk sun halarci filin sauka da tashin jiragen saman na Ilorin.

An ga dawakai dauke da shiri wadanda ke jiran sarkin a kusa da babban asibitin jirgin don shirin hawan daba.

Jami'an tsaro daga hukumar 'yan sanda zuwa jami'an tsaro na farin kaya da NSCDC tare da 'yan banga, duk sun halarci tituna da sakon birnin don tabbatar da doka.

Sarkin Kano Ado Bayero, ya isa garin Ilorin domin gaisuwar ban girma ga Sarkin Ilorin, Mai martaba Ibrahim Sulu Gambari a ranar Juma'a.

Sarkin Kano jika ne a wurin sarki na takwas na Ilorin, Sheikh Abdulkadir Bawa.

Jama'a masu tarin yawa sun yi wa Sarkin Kano maraba a Ilorin (Hotuna)
Jama'a masu tarin yawa sun yi wa Sarkin Kano maraba a Ilorin (Hotuna). Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sojin Mali sun sanar da sakin shugaba Boubacar Keita

Legit.ng ta ruwaito cewa, Sarkin Kano, Alhaji Aminu ado Bayero, zai ziyarci tsohuwar birnin Ilorin mai tarin tarihi a ranar Alhamis, 27 ga watan Augustan 2020, jaridar Solacebase ta wallafa.

Hakan yana daga cikin zagayen rangadi da yake yi a masarautun da ke fadin kasar nan, tun bayan hawan shi karagar sarautar Dabo a watan Maris na wannan shekarar.

Kamar yadda takardar da mai bai wa Sarkin Ilorin shawara na musamman a harkar yada labarai, Mallam Abdulazeez Arowona ya fitar a ranar Litinin, ya tabbatar da wannan ci gaban.

Takardar ta ce, "Nan da ranar Alhamis, 27 ga watan Augustan 2020, Mai martaba, Sarki Ilorin, Alhaji Dr. Ibrahim Sulu Gambari, zai karba bakuncin Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, sarkin Kano.

"Idan ya iso filin sauka da tashin jiragen sama na Ilorin, manyan masu sarauta na masarautar Ilorin za su karbesa da kilisa inda za su shiga da shi cikin birnin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel