Yanzu yanzu: Babban hadimin gwamna El-Rufa'i yayi mumunan hadarin mota a hanyar Abuja/Kaduna
1 - tsawon mintuna
Hafiz Bayero, babban mai bada shawara ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya yi hadarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Litinin.
Har yanzu babu isasshen bayanai game da hadarin amma hoton da jaridar Sahara Reporters ta wallafa ya nuna yadda hadarin ya faru.
Mutanen da ke wajen lokacin sun dauki hoton Bayero da motarsa da lamba 12E-04KD.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Asali: Legit.ng