Sama da daliban makaranta milyan 9 muke ciyarwa - Minista Sadiya

Sama da daliban makaranta milyan 9 muke ciyarwa - Minista Sadiya

Sama da daliban makaratun firamare milyan tara suke amfana da shirin ciyarwa da gwamnatin Buhari ke gudanarwa a fadin tarayya, ministar walwala da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana.

Sadiya ta ce sama da masu girki dubu 100,000 aka dauka aiki domin girkawa daliban abinci a jihohi 34 a fadin tarayya kawo yanzu.

Ministar ta bayyana hakan ne ranar Juma'a a taron murnar shekara daya da kafa ma'aikatar, Daily Trust ta ruwaito.

Ta kara da cewa kafa ma'aikatar ya rage matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa.

A cewarta, kimanin matasan da suka amfana da shirin N-Power 109,823 suka kafa kasuwacin kansu a garuruwansu.

Tace: "Shekara daya kenan yau da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wannan ma'aikatar."

"Shirin ciyar da dalibai da akeyi a jihohi 34 da birnin tarayya yanzu, jimillan adadi daliban da ake ciyarwa yanzu 9,196,823 ne kuma za'a iya tabbatar da hakan wajen hukumar lissafin kasa, yayinda jimillan adadin masu girki ke 103,028."

KU KARANTA: Kamar Jigawa, lauyoyin Bauchi sun yi uwar kungiya bore saboda janye gayyatar El-Rufa'i

Sama da daliban makaranta milyan 9 muke ciyarwa - Minista Sadiya
Sama da daliban makaranta milyan 9 muke ciyarwa - Minista Sadiya
Asali: UGC

A wani labarin mai alaka, Gwamnatin tarayya ta kashe milyan N523.3 wajen ciyar da daliban makarantan firamare a gidajensu lokacin dokar zama a gida sakamakon cutar Coronavirus.

Ministar Walwala, tattalin annoba, da jinkai, Sadiya Farouq, ta sanar da haka ne a zaman hira da manema labaran kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID19 a ranar Litinin a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Sadiya ta bayyana hakan ne domin watsi da jita-jita da raye-rayen da akeyi kan adadin kudin da aka kashe wajen ciyar da yaran lokacin dokar kulle.

Ta ce an sauya fasalin shirin ne kuma aka aiwatar a jihohi uku bisa umurnin da shugaban kasa ya bada ranar 29 ga Maris.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel