ECA: CBN ta gaza yin bayani a kan inda $11bn su ka shige – ‘Yan Majalisa
Majalisar wakilan tarayya ta koka yayin da babban bankin CBN na kasa ya gaza yin bayani game da wasu Dala biliyan 11 da aka zara daga asusun ECA.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an cire wannan kudi ne daga asusun rarar mai na kasa da nufin za ayi wasu ayyukan gyara wutar lantarki a Najeriya, amma abin ya gagara.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, bai iya bada cikakken bayani game da wannan kudi da aka zara ba kamar yadda Akanta-janar ya ke zargi.
Ofishin babban akawun gwamnatin tarayya ya na zargin cewa an cire wannan kudi daga asusun ECA ne tsakanin 2005 zuwa 2007 da nufin yin aikin wuta na NIPPs.
A rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, 13 ga watan Agusta, an bayyana cewa Mista Godwin Emefiele bai gamsar da majalisa game da wannan zargi ba.
KU KARANTA: An jefa Ministan tsaro a badakalar karfa-karfa wajen nadin mukami
Mataimakin gwamnan babban banki, Adebisi Shonubi, ne ya wakilci Emefiele a gaban kwamitin majalisar wakilai da ke gabatar da wannan bincike na musamman.
Kwamitin harkar wutar lantarkin ya ce gwamnati ta iya yin bayanin inda aka batar da Naira tiriliyan 1.51 ne kacal daga cikin wannan kudi da aka ware na aikin wuta.
Binciken da aka yi ya nuna cewa akalla N80b na wannan kudi sun shiga hannun kamfanin NBTE bayan an kammala saida wutar lantarki ga ‘yan kasuwa a Najeriya.
Adebisi Shonubi a madadin gwamnan CBN ya fadawa majalisa cewa FEC ta bada damar a cire N213b, wanda daga ciki an yi amfani da N189.1b zuwa yanzu.
Haka kuma CBN ya amince da fitar da N701b ga ‘yan kasuwa, kuma an yi hakan a 2018. Jimillar kudin da majalisar ta ke ganin sun bi ruwa sun haura N4, 100, 000, 000, 000.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng