Edo: INEC sun karbi hujjojin da ke nuna alamun tambaya a takardun Gani Audu
‘Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar APC, Gani Audu, ya shiga cikin tsaka mai wuya a dalilin zargin rashin gaskiya a kan wasu takardunsa.
A ranar Lahadi, 9 ga watan Agusta, Jaridar Vanguard ta rahoto cewa INEC ta karbi wasu takardu da ke zargin Mista Gani Audu da yin karya a game da satifiket dinsa.
Takardun da aka mikawa hukumar zabe na kasa ta INEC sun nuna tun farko akwai kwan-gaba-kwan-baya game da sunan ‘dan takarar da kuma takardun shaidar da ya bada.
An samu wannan matsala ne a wasu takardun Gani Audu wanda hakan na iya jawowa jam’iyyar APC mai hamayya ta rasa kujerar gwamnan jihar Edo, ko da ta yi nasara a zaben.
A dalilin karya game da takardun makarantar ‘dan takarar mataimakin gwamnan da jam’iyyar APC ta tsaida a zaben jihar Bayelsa ne ta rasa mulki, duk da ta lashe zaben da aka yi.
Karin matsalar da Gani Audu ya shiga shi ne, jam’iyyar ADP mai hamayya ta shigar da kara a gaban kotun tarayya da ke Abuja, ta na rokon a hana ‘dan takarar tsayawa zabe.
KU KARANTA: Ana neman kashe ni - Mataimakin Gwamnan Edo
Jam’iyyar adawar ta bukaci Alkali ya tabbatar da cewa Audu ya yi wa hukuma karya game da takardunsa, don haka bai da damar tsayawa takarar kujerar mataimakin gwamna.
‘Dan takarar na APC ya bada takardar rantsuwar kotu da ta bayyana sunansa a matsayin Audu Abudu Ganiyu, amma kuma wasu satifiket dinsa sun ci karo da wannan suna.
Blessed Omonuwa, Lauyan da ya duba hujjojin da aka mikawa INEC, ya ce sunan da ke jikin katin zaben Audu dabam da abin da ya zo cikin katinsa na zama ‘dan jam’iyyar APC.
Kamar yadda Lauyan ya bayyana, wannan karya ta sabawa sashe 182 (1) (j) na kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999, kuma babu yadda za a iya mutum ya samu sunaye biyu.
“Bayanin kawai da za a iya yi shi ne, watakila ya yi amfani ne da takardun karatun wani mutum dabam.” Masanin shari’ar ya ce APC na iya fuskantar irin abin da ya faru a Bayelsa a zaben Edo.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng