Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya fara ganawa da mambobin kungiyar gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress APC ta yanar gizo, The Nation ta samu rahoto.

An kaddamar da ganawar misalin karfe 11:25 na safiyar yau.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, kadai ne wanda ke tare da Buhari a mutum yayinda sauran su shiga ta yanar gizo.

Sauran wadanda ke zaman sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Har yanzu da muke tattara labarin ba'a gano dalilin ganawar ba.

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC
Asali: UGC

Ku saurari cikakken rahoton....

Asali: Legit.ng

Online view pixel