Da duminsa: Akalla 7 sun mutu yayinda motar yan sanda tayi hadari a kanyar Zaria

Da duminsa: Akalla 7 sun mutu yayinda motar yan sanda tayi hadari a kanyar Zaria

Da yiwuwan mutane bakwai sun rasa rayukansu a mumunan hadarin mota da ya auku ga jami'an sanda da aka yiwa horo na musamman watau 'special forces' a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ba'a san abinda ya sabbaba hadarin ba.

Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa hadarin ya auku misalin karfe 4:30 na la'asar, kusa da barikin Sojin Jaji, inda mota dauke yan sanda tayi kuli-kulin kubura.

Wani direban motar haya 'Sharon' da ya shaida hadarin, Hassan, ya bayyana cewa: "Mumunan hadari ne saboda na kirga kimanin gawawwakin yan sanda bakwai a tsakiyar titi."

"Wasu biyu sun yi mugun jikkata yayinda sauran suna tsira."

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda, ASP MUhammad Jalige, ya ce an tua yan sanda wajen ganin ainihin abinda ya faru.

Da duminsa: Akalla 7 sun mutu yayinda motar yan sanda tayi hadari a kanyar Zaria
Da duminsa: Akalla 7 sun mutu yayinda motar yan sanda tayi hadari a kanyar Zaria
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel