Zaman tsige mataimakin gwamna: 'Yan sanda sun mamaye harabar majalisar Ondo

Zaman tsige mataimakin gwamna: 'Yan sanda sun mamaye harabar majalisar Ondo

'Yan majalisar jihar Ondo sun fara shirin tsige mataimakin gwmanan jihar, Mr Agboola Ajayi.

A halin yanzu yan majalisar na tattaunawa a zauren majalisar a kan zargin saba dokokin aiki da ake yi wa mataimakin gwamnan.

Bayan tattaunawar, Majalisar ta cimma matsayar aike wa mataimkin gwamnan takardar sanar da tsige shi

Zaman tsige mataimakin gwamna: 'Yan sanda sun mamaye harabar majalisar Ondo
Zaman tsige mataimakin gwamna: 'Yan sanda sun mamaye harabar majalisar Ondo. Hoto daga TVC
Asali: UGC

Jami'an 'yan sanda da na hukumar tsaro ta NSCDC sun mamaye harabar majalisar domin tabbatar da doka da oda.

DUBA WANNAN: An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)

An hana 'yan jarida shiga harabar majalisar. An bukaci su kira Gbenga Omole, shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar ya basu izini kafin a bari su shiga kamar yadda The Cable ta ruwaito.

'Yan majalisa ne kawai da maaikatan majalisar aka bari suka shiga harabar majalisar.

Ajayi ya fice daga jamiyyar All Progressives Congress (APC) ya koma jamiyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma ya bayyana cewa zai tsaya takarar gwamna a PDP a watan Oktoba.

Hakan na nuna zai fafata da tsohon mai gidansa kuma gwamnan mai ci a yanzu Oluwarotimi Akeredolu.

Gwamna Akeredolu ya sallami dukkan maaikata da hadiman da ke aiki karkashin ofishin Ajayi ya kuma janye 'yan sanda da sauran jami'an tsaro masu tsaron lafiyarsa har sai da Sufeta Janar na 'Yan sanda, Mohammed Adamu ya shiga tsakani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel