Yanzu-haka: Buhari yana jagorantar taron FEC ta intanet (Bidiyo)
Shugaba Muhammadu Buhari a halin yanzu yana jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, da ake gudanarwa a dakin taro na Majalisar da ke Fadar shugaban kasa a Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha; Shugaban Maaikatan Fadar Shugaban Kasa, Prof. Ibrahim Gambari; da Mai bawa Shugaban kasa shawara a kan tsaro, Babagana Monguno.

Asali: UGC
Saura sun hada da Attoney Janar na kasa kuma ministan Sharia, Abubakar Malami; Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsare Tsaren kasa, Zainab Ahmed; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fasola; Ministan Labarai da Alaadu, Lai Mohammed; da Ministan harkokin Sufurin Jiragen Sama, Senator Hadi Sirika.
Ga bidiyon yadda taron ke gudana a kasa
Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Malam Muhammed Bello da Ministan Albarkatun Ruwa, Injiniya Suleiman Adamu suma sun hallarci taron.
Mahalarta taron sun zauna ne da tazara tsakaninsu tare kuma da saka takunkumin rufe fuskokinsu kamar yadda hukumomin lafiya suka bayar da shawarwari a wannan yanayi na annobar korona.
Ku saurari karin bayani ...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng