Katsina: Yadda 'yan gudun hijira suka dinga kuka bayan Masari ya kai ziyara

Katsina: Yadda 'yan gudun hijira suka dinga kuka bayan Masari ya kai ziyara

- Mata da yara a sansanin yan gudun hijira da ke Faskari a jihar Katsina sun rushe da kuka yayin da Gwamna Aminu Masari da wasu manyan jiga-jigan gwamnati suka kai ziyara sansanin

- Sun nemi a kawo masu agaji ta hanyar tallafa masu sakamakon ibtila'in da ya saukar masu

- Yan gudun hijirar sun bukaci a samar da zaman lafiya ta yadda za su samu damar komawa gidajensu

- Masari ya ce ya shiga damuwa matuka a kan rashin tsaron jihar tare da tabbatar da cewa za a mayar da hankali wurin komawarsu gida

Da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijira da ke Faskari a jihar Katsina sun rushe da kuka yayin da gwamna Aminu Masari da wasu manyan jiga-jigan gwamnati suka kai ziyara sansanin.

Sun bukaci tallafi sakamakon ibtila'in da ya fada musu.

Yara da mata sun fashe da kuka bayan da gwamnan tare da manyan jami'an gwamnati suka bar sansanin bayan ziyarar.

Suna ta ihun neman taimako tare da tallafi musamman ta bangaren samar da zaman lafiyan da zai sa su koma gidajensu.

Katsina: Yadda 'yan gudun hijira suka dinga kuka bayan Masari ya kai ziyara
Katsina: Yadda 'yan gudun hijira suka dinga kuka bayan Masari ya kai ziyara Hoto: Independent Newspapers
Asali: UGC

Wasu daga cikin matan sun dora hannuwansu a kai yayin da wasu ke faduwa kasa suna kuka.

Akwai a kalla mata da kananan yara 3,886 a sansanin. Zaman sansanin ya zame musu dole bayan harin da 'yan bindiga suka kai musu wanda ya kawo mutuwar da yawa daga cikin su tare da salwantar kadarorinsu.

A yayin jawabi garesu, Masari ya ce ya shiga damuwa matuka a kan rashin tsaron jihar tare da tabbatar da cewa za a mayar da hankali wurin komawarsu gida.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: NNPC ta sanar da samun man fetur a wata jihar arewa

Ya ce: "Yan bindigar basu san komai ba da ya wuce karfin bindiga kuma akwai bukatar a yi amfani da hakan wurin maganinsu. Ba za su iya zama daya da dakarun sojinmu ba.

"Dole ne jama'a su samar da bayanai masu amfani ga jami'an tsaro don kawo karshen matsalar. Muna rokonku da ku yi hakuri da mu," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng