Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina (hotuna)

Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina (hotuna)

Dandazon jama’a a jihar Katsina sun fito domin yin zanga-zanga a kan hauhawan rashin tsaro a fadin jihar.

Masu zanga-zangar sun kawar da shingen da jami’an yan sanda suka sanya a manyan tituna yayin gudanar da tattakin nasu, Sahara Reporters ta ruwaito.

A wani sakon murya da majiyar Legit.ng ta samu, an jiyo daya daga cikin jagororin zanga-zangar mai suna Kwamrad Usman Hussaini Rafuka yana fadin cewa:

“Musababbin wannan zanga-zangar da muka shirya, kowa dai ya sani musamman indai mutum yana a yankin arewacin Najeriya, ya san menene musababbin.

“Musababbinta bai wuce yanayin yadda ake kisan al’umma, musamman idan kika dauki jihar Katsina, muna da kananan hukumomi kusan 15 wanda a kullun sai an zub da jini a wannan yankin.

“Da wuya ka ji an ce ba a kashe mutum 20 ba kai har mutum 100 ana kashewa a rana daya.

Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina (hotuna)
Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina Hoto: Shahara Reporters
Asali: Facebook

“Yanzu haka maganar da nake yi da safe akwai wanda yana daga cikin masu wannan zanga-zangar lumanan da muka shirya, wanda da safen nan na kira shi ya batun tafiya sai yake ce mun wallahi yanzu haka a jiya a Batsari akwai wani gari an shiga an tafi da kanin mahaifinsa.

“Wannan ne dalilin da yasa ma ba zai samu halartan zanga-zangar ba. Kin ga kenan shi abun dake faruwa a jihar ya ma shafe shi.

“Kuma idan aka shiga irin wannan wuraren ana kashe mutane sannan a tafi da wasu, matansu ma a gaban ‘ya’ya da miji ayi masu fyade, idan an gama ma sai su dibi rowan batir su watsa ma mace. Shin mai ya fi wannan bala’i? Kuma ma ina manyanmu na arewa? Mun ji sun yi shiru.

“Kwanan nan naga wani bidiyon dattawan arewa na nuna gazawar gwamnatin nan, saboda bata cika alkawari, abu na farko tace za ta bayar da tsaro amma duk ta gaza.

“Kafin ma wannan zanga-zangar mun tura wa hukumomin tsaro cewa za mu yi zanga-zangar lumana ne, akwai kungiyoyi na sa-kai akwai kungiyoyin dalibai da makamantansu, amma daga karshe an nemi a wurga da mutane.

“Maganar da nake yi maka, yanzu haka mintina 41 a ofishin yan sanda a bayan kanta, an kama mu, wanda mun gaya masu abunda za mu yi, amma sai aka kulle hanyoyi, ba a bamu hadin kai ba, wanda yan sanda na lamba daya wajen rashin bamu hadin kai.

“Sai dai daga baya sun bamu hadin kai na maganganu, domin shi kansa kwamishinan ya zo, domin da bai zo ba da Shugaban yankin ba zai sake mu ba, an kamamu mu hudu tsawon minti 41.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Jama'a za su fito zanga-zanga a fadin jihar a kan kashe-kashen 'yan bindiga

“Kuma mu zanga-zangar luma muke yi kuma muna yin sa saboda talaka ne domin mu talakawa ne, ana kashe mana yan’uwanmu. Akalla mutane 300 zuwa 400 ne suka fito zanga-zangar tsakanin maza da mata."

Ga karin hotunan zanga-zangar a kasa:

Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina (hotuna)
Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina Hoto: Shahara Reporters
Asali: Facebook

Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina (hotuna)
Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina Hoto: Shahara Reporters
Asali: Facebook

Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina (hotuna)
Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina Hoto: Shahara Reporters
Asali: Facebook

Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina (hotuna)
Jama'a sun kawar da shingen 'yan sanda yayin zanga - zanga a Katsina Hoto: Shahara Reporters
Asali: Facebook

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel