Jaririn wata 3 ya sullubo daga hannun mahaifiyarsa a ginin saman Asibiti a Abuja

Jaririn wata 3 ya sullubo daga hannun mahaifiyarsa a ginin saman Asibiti a Abuja

Wani jariri mai wata uku (3) da haihuwa ya rasa rayuwarsa sakamakon sullubowa daga ginin sama na asibitin Garki dake kwaryar birnin tarayya Abuja, jaridar Punch ta samu labari.

Labarin ya bayyana cewa hadarin ya faru ne da safiyar Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2020.

Wani mai gadi a asibitin ya bayyanawa manema labarai cewa mahaifiyar jaririn da wasu mutane biyu dake tare da ita suna hanyar shiga cikin asibitin ne abin ya faru.

Yace: "Wata mata da wasu biyu na sama, sun gudu zuwa sashen jinyar gaggawa, yayinda jaririn da take dauke da shi ya sullubo daga hannunta ya fado kasa."

"Wuyan jaririn ya karye kuma ya mutu nan take."

Jaririn wata 3 ya fado daga benen sama a Asibitin Abuja, ya mutu
Jaririn wata 3 ya fado daga benen sama a Asibitin Abuja, ya mutu
Asali: Facebook

Shugaban asibitin, Dr. Adamu Onu, ya ki magana yayinda aka tuntubesa yayi tsokaci.

Yayinda aka tambayeshi shin ya tuntubi jami'an yan sanda, shugaban asibtin ya ce mutane na da hurumi kan lamuransu saboda haka ba zai bayyanawa yan jarida komai ba.

Yace: "Hadari ya faru a asibiti amma ba abu bane da zan iya fallasawa ba saboda hakkin marasa lafiya."

"Ba zan iya muku wani magana fiye da abin da na fadi ba."

KU KARANTA: Ambaci sunayen Sarakunan gargajiyan da ke taimakawa yan bindiga a Katsina - An bukaci Garba Shehu

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sandan birnin tarayya, Anjuguri Manza, ya ce bai samu labari ba kuma ba'a kawo musu labari ba.

Yace: "Ban tunanin an kawo wa yan sanda wannan lamarin. Ku tambayi asibitin idan sun kai kara ofishin yan sanda mafi kusa da su."

A wani labarin daban, Daily Trust ta bada rahoton yadda akayi wa jaririya mai watanni uku fyade a kauyen Adogi da ke jihar Nasarawa, jaridar ta wallafa.

A halin yanzu, jaririyar tana asibitin koyarwa na jami'ar Jos inda take samun taimako daga masana kiwon lafiya.

Maimuna Adam, mahaifiyar jaririyar ta sanar da Daily Trust a Jos cewa lamarin ya faru ne a daren ranar 27 ga watan Mayu, yayin da suke bacci amma kofarsu ke bude sakamakon zafin da ake yi a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel