Dan Atiku ya karyata fadin cewa mahaifinsa zai yi takarar shugaban kasa a 2023

Dan Atiku ya karyata fadin cewa mahaifinsa zai yi takarar shugaban kasa a 2023

- Adamu Abubakar ya soki rahoton kafofin watsa labbarai da ke ikirarin cewa ya ce mahaifinsa zai yi takarar zaben shugaban kasa a 2023

- Adamu wanda ke matsayin kwamishanan ayyuka da makamashi a jihar Adamawa ya bayyana cewa ba a fahimci maganarsa ba

- Kwamishinan ya ce kawai yana kokarin jan bambanci ne tsakanin matsayin siyasarsa da na mahaifinsa

Adamu Abubakar, babban dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya karyata fadin cewa mahaifinsa zai tsaya takarar zaben shugaban kasa a 2023.

Adamu wanda ke a matsayin kwamishinan ayyuka da makamashi na jihar Adamawa ya bayyana cewa kafofin watsa labarai sun sauya maganarsa kan lamarin, jaridar Tribune ta ruwaito.

“Yan jaridan sun sauya maganata kuma ba abunda nake nufi ba kenan,” in ji Adamu.

Dan Atiku ya karyata fadin cewa mahaifinsa zai yi takarar shugaban kasa a 2023
Dan Atiku ya karyata fadin cewa mahaifinsa zai yi takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa yana kokarin jan bambanci ne tsakanin matsayin siyasarsa da na mahaifinsa ne kawai.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A cewar Adamu, abunda yake nufi shine cewa ya fito ne daga ahli na siyasa inda mahaifinsa ya gina wa kansa kogo na siyasa, a kundin tsarin mulki, yana da ikon tsayawa takara a kowani yanayi.

Kafofin watsa labarai sun rahoto cewa Adamu Abubakar ya ce mahaifinsa zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

A cewar jaridar The Nation, an ce Adamu ya yi furucin ne a lokacin wani taro da aka gudanar domin raya shekarar farko da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya yi a kan mulki.

Hakazalika shi kansa Adamu Atiku-Abubakar ya shafe shekara guda kenan a ofis a matsayin kwamsishinan ayyuka.

Ya kuma bayyana mahaifinsa a matsayin "kwararren ‘dan siyasa, mai dabara, uban gida, wanda ya kuma lakanci harkar siyasa na kusan shekaru 40."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Lawan ya yi wa Kalu maraba da dawowa majalisar dattawa

Mun dai ji cewa Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tsarin karba - karba ne kadai zai nuna makomar yiwuwar takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

An fara maganganu a kasa a kan cewa Atiku zai fito takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel