Bayan samun sabon bulla 2 a Kebbi, Almajirai daga Kaduna sun kai 11 Sokoto

Bayan samun sabon bulla 2 a Kebbi, Almajirai daga Kaduna sun kai 11 Sokoto

Bayan kimanin mako daya da karewa cugar Korona a jihar Kebbi, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da samun bullar cutar a jihar Kebbi.

A jihar Sokoto kuwa, kwanaki biyu kacal bayan sanar da karewar cutar, an samu karin mutane 12 sabbin kamuwa da cutar.

Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana a yau 6 ga watan Yunin 2020, an samu sabbin masu cutar korona 389 a Najeriya.

A jihar Legas an samu karin mutum 66 da ke dauke da muguwar cutar, yayin da babban birnin tarayya na Abuja ke biye da sabbin mutum 50.

A jihar Sokoto, an samu sabbin bulla goma sha daya (11) yayinda aka samu sabbin bulla biyu (2) a jihar Kebbi.

Ma'aikatar lafiyar jihar Sokoto ta bayyana cewa Almajiran da aka kawo daga jihar Kadina 33 da aka samu sabbin masu cutar a jihar.

Jawabin yace, "Kwamitin yakar cutar COVID-19 ta karbi Almajirai 33 da aka kawo daga Zaria jihar Kaduna ranar 4 ga Yuni, 2020."

"Dukkan Almajiran 33 na killace a sansanin NYSC dake Wamakko kuma yayinda suka isa jihar muka dauki samfurinsu."

"Amma kash! 11 cikin wadannan 33 sun kamu da cutar."

A ranar Asabar, mun kawo muku jerin jihohi uku da suka sallami dukkan masu fama da cutar Koronansu amma da alamun yanzu jiha daya kadai ta rage.

Jihar Zamfara ce wacce ta fara sanar da karewar cutar ranar 28 ga Mayu, 2020 kuma har yanzu ba'a sake samun mai cutar ba.

Kwanaki cutar Korona 100 yanzu a Najeriya kuma an samu akalla mutane 12,000 da suka kamu da cutar. Yayin da mutum 3826 suka warke daga jinyar cutar. Mutum 342 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon annobar da ta zagaye duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel