Yanzu-yanzu: Hukumar kula da alamuran 'yan sandan Najeriya ta yi babban rashi

Yanzu-yanzu: Hukumar kula da alamuran 'yan sandan Najeriya ta yi babban rashi

Wakilin hukumar kula da al'amuran 'yan sandan Najeriya (PSC) na yankin Kudu maso gabas, Dr Jumbo Nkemka Offor ya rasu.

Offor ya rasu a ranar Laraba da dare a gidansa na Enugu da ke yankin Osimiri Lodge.

Har a halin yanzu ba a gano dalilin mutuwarsa ba, jaridar The Nation ta wallafa.

Offor kwararren likita ne wanda ya fito daga yankin Arochukwu da ke jihar Abia. Ya fada al'amuran kasuwanci tun bayan kammala karatunsa.

Shine shugaban ma'aikatar kasuwanci, masana'antu, hakar ma'adanai da noma da kiwo (ECCIMA) na jihar Enugu.

Shi ya shirya shagalin '99 World Youth Soccer da aka yi a Najeriya.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel