Yadda wata mata ta yi wa jami'an PHCN mugun duka da yaje karbar wuta ana kulle (Bidiyo)

Yadda wata mata ta yi wa jami'an PHCN mugun duka da yaje karbar wuta ana kulle (Bidiyo)

- Wata fusatacciyar mata ta yi wa jami'an hukumar wutar lantarki ta kasa mugun duka bayan sun je karbar kudin wuta

- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, ma'aikatan sun je dauke da tsani za su gutsire musu wuta saboda basu biya ba duk da kuwa dokar kulle da ke aiki

- Matar mai kamar maza ta kama jami'in na farko inda tayi masa jina-jina sannan ta damko na biyun tare da rufe shi da duka

Wani bidiyo da ke bayyana yadda wata mata ta yi wa jami'an hukumar wutar lantarki ta Najerya mugun duka ya jawo cece-kuce, jaridar The Nation ta wallafa bidiyon.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, jami'an sun bayyana dauke da tsani da niyyar cire wutar lantarkin gidajen saboda basu biya ba.

Lamarin ya matukar harzuka matar don kuwa a halin da ake ciki babu mai fita sana'a ballantana a samu kudin biya.

Bayan cacar bakin da aka yi tsakaninta da jami'an, an ganta ta hau daya daga ciki da duka babu ji balle gani. Tuni kuwa yace 'kafa me naci ban baki ba'.

Ba ta kakkauta ba ta hada da dayan jami'in mai sanye da hula kuma rike da tsani ta fara dukan shi. Bai yi kasa a guiwa ba shima ya san inda dare yayi masa.

KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriyasun tarwatsa ma'adanar makaman 'yan ta'adda a Borno, sun bi ta wani da motar yaki (Bidiyo)

A wani labari na daban, farmakin da sojin saman Najeriya karkashin rundunar Operation Lafiya Dole ta kai a Njimia da ke dajin Sambisa, ya tarwatsa kayan yakin 'yan ta'addan Boko Haram.

Hari ta jiragen saman yakin da dakarun suka kai a ranar Talata ya biyo bayan rahotannin sirrin da suka samu a kan makaman 'ya ta'addan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda bayanan suka nuna, wurin adanar makaman na nan a kusa da inda mayakan ke amfani da shi a matsayin sansani. Suna ajiye man fetur da sauran kayayyakin bukata, kamar yadda takardar da Manjo Janar John Enenche ya fitar ta bayyana.

Ya ce babu kuskure harin da suka kai ya samu inda suka saita tare da tashin yankin. A take kuwa ma'adanar makaman suka kurmushe tare da yin mummunar barna ga mazaunin 'yan ta'addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel