COVID-19: An killace ‘Yan Majalisar Tarayya da wasu Ministoci a Chile

COVID-19: An killace ‘Yan Majalisar Tarayya da wasu Ministoci a Chile

Rahotanni daga gidan yada labaran AFP sun tabbatar da cewa kusan rabin sanatocin kasar Chile da ministocin kasar aka killace bayan sun yi alaka da masu dauke da cutar COVID-19.

A ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2020, jami’an kasar Chile da ke nahiyar Amurka ta kudu su ka bayyana cewa an yi wa ‘yan siyasan gwaji, amma ba a same su dauke da cutar ba.

Likitoci sun tabbatar da cewa an samu ‘yan majalisa da ministocin kasar uku da su ka kamu da cutar. Ana kuma jin tsoron wadannan manyan kasa su yi sanadiyyar yada cutar.

AFP ta ce yanzu wadannan ‘yan siyasa su na killace kuma ba za a fito da su ba har sai an sake yi masu wani gwaji domin a tabbatar da cewa babu wanda kwayar cutar ta harba.

Likitoci su kan yi wa wanda ake zargin ya kamu da cutar gwaji sau biyu a jere kafin a tabbatar da matsayar lafiyarsa. A daidai wannan lokaci kasar Chile ta na fama da zanga-zanga.

KU KARANTA: COVID-19 ta kashe Fasto mai warkar da masu Coronavirus

Marasa karfi a Chile su na neman gwamnati ta taimaka masu da kayan abinci. Wannan har ya kai ga mummunar boren da sai da gwamnati ta baza jami’an tsaro a garin Santiago.

Ministan kudin kasar, Ignacio Briones da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Felipe Ward, sun fito shafin Tuwita sun shaidawa Duniya cewa cutar COVID-19 ba ta harbe su ba.

Briones ya ce an yi masa gwaji a ranar Juma’ar da ta gabata ne bayan ya hadu da sanata Jorge Pizarro mai dauke da ciwon, a wajen wani zaman kwamitin tattalin arziki da su ka yi.

Sanatoci kusan 25 daga cikin ‘yan majalisar dattawa 50 na kasar Chile aka killace. Sauran ministocin gwamnatin da ke tsare su ne na harkokin gida da na cigaban al’umma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel