Hukumar Kwalejin horas da hafsoshin Soji ta kai ma jama’an Kano da Jigawa dauki
Kwalejin horas da hafsoshin Sojin Najeriya, NDA Kaduna, ta kai gudunmuwar ruwan wanke hannu na Hand Sanitizer ga gwamnatocin jahohin Kano da Jigawa don yaki da COVID19.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito kakaakin kwalejin, Manjo Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar Talata, 5 ga watan Mayu a garin Kaduna.
KU KARANTA: Gwamnan Katsina ya bayyana abin da yasa gwamnati ta garkame fadar masarautar Daura
Abdullahi ya ce kwalejin ta dauki wannan mataki ne don bayar da gudunmuwarta ga rage yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya tare da kawo karshensa a kasar.
Abubakar ya ce rajistran kwalejin, Birgediya Ayoola Aboaba ne ya mika kayan a garin Kano da Dutse, inda yace manufar gudunmuwar shi ne taimaka ma kokarin da gwamnatocin suke yi.

Asali: UGC
Ayoola ya tabbatar ma gwamnatocin biyu cewa a sashin ilimin Chemistry na kwalejin ne suka sarrafa sinadarin, kuma sun samu amincewar hukumar NAFDAC, da bin ka’idojin WHO.
Haka zalika kakaaki Abubakar ya kara da cewa kwalejin na da kudurin raba tallafin ga sauran jahohin dake makwabtaka da su don samar da kyakkyawar alaka tsakanin Soja da farar hula.
Guda daga cikin manyan sakatarorin jahar Kano, Idris Dawakin Tofa ne ya amshi kayan a madadin gwamnatin, kuma ya bayyana farin cikinsa ga kwalejin bisa wannan tallafin.
Shi ma kwamishinan kiwon lafiya na jahar Jigawa, Abba Zakari ya bayyana farin cikinsa da godiyansa ga kwalejin NDA, sa’annan yayi addu’an Allah Ya kawo karshen annobar.
A wani labari kuma, Ma’aikatan kiwon lafiya guda 14 sun kamu da annobar cutar Coronavirus a jahar Katsina, kamar yadda gwamnan jahar, Aminu Bello Masari ya tabbatar.
Masari ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, inda yace ma’aikatan na daga cikin sabbin mutane 37 da suka kamu da cutar daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Mayu a jahar.
Wanda ya fara mutuwa daga cutar shi ne Dakta Aliyu Yaukubu, babban likita a garin Daura, kuma shi ya fara kamuwa da cutar bayan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa jahar Legas.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng