'A fusace na ke a lokacin' - Dattijon da aka kama saboda ya zagi Buhari ya yi bayani

'A fusace na ke a lokacin' - Dattijon da aka kama saboda ya zagi Buhari ya yi bayani

Lawal Izala, wani dattijo mai shekaru 70 da aka kama saboda zagin shugaban kasa, Muhammdu Buhari, ya ce ya yi zagin ne cikin fushi bayan 'yan bindiga sun kai hari kauyensu tare da kashe 'yan uwansa da sace shanunsa 15.

A ranar Alhamis ne rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da kama wasu mutane uku da su ka zagi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

An kama mutanen ne bayan wani faifan bidiyonsu da su ke zagin shugabannin ya kewaya a dandalin sada zumunta.

Mutanen uku da aka kama sun hada da wani dattijo dan shekara 70 mai suna Lawal Abdullahi Izala, da Bahhajje Abu, da Hamza Abubakar, dukkansu mazauna unguwar Gafai a cikin garin Katsina.

A cewar dattijon mai shekaru 70, "ina cikin tafiya aka tsayar da ni aka tamabyeni ya rayuwa, lokacin na dawo kenan daga kauye bayan 'yan bindiga sun kai hari, sun kashe 'yan uwana, sun sace min shanu 15.

"Sai na ce shugabanninmu; Buhari da Masari, sun ci amanar mu. Shine na yi zage-zage cikin fushi da bacin rai ba tare da sanin cewa ana nada a bidiyo ba.

"Ni kawai ina fadin gaskiyar abinda ke raina ne. Bayan faifan bidiyon ya zagaya a dandalin sada zumunta, sai 'yan sanda su ka kamani. An zargeni da aikata laifi a karkashin kundin tsarin mulki."

Rahotanni na yawan kawo labaran yadda 'yan bindiga ke cigaba da kai hare - hare tare da cin karensu babu babbaka a kauyukan jihar Katsina, musamman a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Rundunar 'yan sanda ta cigaba da tsare mutanen uku ba tare da basu zabin samun beli ba.

'A fusace na ke a lokacin' - Dattijon da aka kama saboda ya zagi Buhari ya yi bayani
Dattijo da mutane biyu da aka kama saboda zagin Buhari
Asali: Twitter

Da ya ke magana yayin holin mutanen uku, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce an karar da rundunar 'yan sanda a kan wani faifan bidiyo da wani da aka fi sani da 'Izala', ya ke zagin Buhari da Masari a cikinsa.

DUBA WANNAN: Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC

"A Saboda haka, kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, CP Sanusi Buba, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, wanda ya kai ga an kama mutanen uku," a cewarsa.

Ya kara da cewa, "a yayin da mu ke tuhumarsu, wadanda ake zargi sun amsa laifinsu.

"Ya kamata jama'a su sani cewa rundunar 'yan sanda ba za ta nade hannayenta tana kallon wasu tsirarun marasa tarbiyya suna sabawa dokokin kasa ba.

"Duk wanda aka samu ya na amfani da dandalin sada zumunta domin zagin wani mutum ko wasu mutane, zai fuskanci fushin doka, kamar yadda aka tanada a karkashin dokokin hukunce - hukuncen manyan laifuka a yanar gizo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel