Dokar kulle: Matasa sun yi wa jami'an tsaro ruwan duwatsu a kasuwar Kaduna

Dokar kulle: Matasa sun yi wa jami'an tsaro ruwan duwatsu a kasuwar Kaduna

An samu rudani a kasuwar Barci da ke Tudun Wada yayin da wasu fusatattun matasa suka jefi jamian tsaro da suka zo kasuwa suna korar mutanen da ke sayar da kayayyakin da gwamnati ba ta halasta siyarwa ba sakamakon dokar kulle ta Covid-19.

Lamarin ya faru ne a kan layin Ibrahim Taiwo road inda masu sayar da gwanjo suka baza kayayyakin su.

An gano cewa motocin jamian tsaro biyu ne suka iso kasuwar misalin karfe 12 na rana suka fara umurtar masu sayar da gwanjon su kwashe kayayyakin su su koma gida.

Dokar kulle: Matasa sun yi wa jami'an tsaro ruwan duwatsu a kasuwar Kaduna
Dokar kulle: Matasa sun yi wa jami'an tsaro ruwan duwatsu a kasuwar Kaduna. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Wani mai sayar da kayan gwanjo, "Wasu abokan aikin mu sun fara kwashe kayansu, sai wasu yan daba suka fara ihun “karya ne “karya ne” su kuma jamian tsaro suka fara kokarin kwace wayoyin da suke daukan su bidiyo da shi.

"Daga bisani, wasu yara suka fara jifan jamian tsaron da duwatsu hakan ya tilasta musu barin kasuwan a cikin motocinsu."

DUBA WANNAN: An kori ma'aikata 46 a kamfanin Atiku a ranar ma'aikata ta duniya

Wani mai sayar da kayan masarufi Bello Idris ya ce an shiga rudani yayin da matasan suka far jifan jami'an tsaron.

Ya ce, "An shiga rudani saboda wasu masu sayar da kaya da masu shaguna sun rufe shagunan su sun fara gudu lokacin da matasan ke jifan jami'an tsaron."

An gano cewa jamian tsaron sun kama mutum daya a lokacin da ake hayaniyar.

Wani jami'in KASTELEA da baya son a fadi sunansa ya ce ana ta jifar jamian tsaron kusa da shataletalen Tudun wada da ke kusa da inda abin ya faru.

Ya ce, "Eh, matasa sun jefi jami'an tsaro da duwatsu kusa da kasuwa domin ina iya ganin duwatsu masa yawa a kasa."

Daily Trust ta ruwaito cewa tuni dai hankula sun kwanta amma wasu masu shaguna sun rufe shagunansu sun tafi gida.

Kakakin yan sandan jihar, ASP Jalige ya ce zai bincika lamarin kafin ya yi jawabi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel