Shugabanin APC na jihohi sun bayar da shawarar yadda za a zabi magajin Abba Kyari

Shugabanin APC na jihohi sun bayar da shawarar yadda za a zabi magajin Abba Kyari

Kungiyar shugabanin jihohi na jamiyyar APC ta bukaci shugabanin jam'iyyar na kasa su zaba wa Shugaba Muhammadu sabon shugaban ma'aikatan fadarsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa tuni dai an fara shirye shiryen zaben wanda zai cike gurbin da marigayi Abba Kyari ya bari na shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Wannan shawarar da kungiyar ta bayar yana dauke ne cikin wasikar da ta aike wa shugaban kasar na ta'aziyar rasuwar Abba Kyari.

Shugaban kungiyar, wanda shine kuma shugaban APC na jihar Borno, Ali Bukar Dalori ne ya rattaba hannu a kan sanarwar.

Shugabanin APC na jihohi sun bayar da shawarar yadda za a zabi magajin Abba Kyari
Shugabanin APC na jihohi sun bayar da shawarar yadda za a zabi magajin Abba Kyari
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta fadi dalilan da yasa ta rufe kamfanin shinkafa na Tiamin

A cewarsa, rasuwar Abba Kyari zai shafi shugabanin jamiyyar duba da cewa marigayin ne ke sada shugabanin jam'iyyar da shugaban kasa.

Dalori ya ce rasuwar Abba Kyari darasi ne ga yan Najeriya kan batun zama a gida saboda coronavirus duba da cewa cutar na iya kisa ko da mutum ya samu kulawar likitoci.

Ya kuma ja kunnen wadanda suke kokarin neman kujerar marigayi Abba Kyari su sani cewa kujera ce wadda ke da muhimmanci wurin taimakawa shugaban kasa cimma manufofinsa.

Kungiyar ta ce, "Muna mika ta'aziyar mu ga gwamnatin Borno, jam'iyyar AC ta Borno da iyalan mammacin.

"Yana da muhimmanci wadanda ke neman kujerar Abba Kyari su sani cewa aiki ne da wanda shugaban kasa ya amince da shi, don ya taimaka masa cimma manufofinsa.

"Kungiyar ta yi kira ga shugabanin jamiyyar su san yadda za su taimakawa shugaban kasa idan da hali su zaba masa wanda zai zama shugaban maaikatan fadar shugaban kasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel