Gwamnatin Kano ta fadi dalilan da yasa ta rufe kamfanin shinkafa na Tiamin

Gwamnatin Kano ta fadi dalilan da yasa ta rufe kamfanin shinkafa na Tiamin

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano, Dr Kabiru Getso ya ce gwamnatin jihar ta rufe kamfanin Shinkafa na Tiamin ne a jihar saboda kusancin ta da wurin killace masu cutar Covid-19 da ke Kwanar Dawakin Kudu.

Mr Gesto ya yi wannan jawabin ne bayan ikirarin da kamfanin ta yi na cewa ba ta aikata laifi ba da zai saka a rufe ta kuma ta yi barazanar kai kara kotu a kan batun.

Kwamishinan ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labarai, NAN, a ranar Litinin a Kano cewa tun a baya gwamnati ta gargadi kamfanin a kan yadda ta ke gurbata muhalli a unguwar.

Ya ce an yi wa kamfanin gargadin ne sakamakon korafi da mutanen da ke zaune kusa da kamfanin su kayi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnatin Kano ta fadi dalilan da yasa ta rufe kamfanin shinkafa na Tiamin

Gwamnatin Kano ta fadi dalilan da yasa ta rufe kamfanin shinkafa na Tiamin
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Mun killace wadanda ake zargin suna dauke da cutar a Otal — Ganduje

Mr Getso ya ce, "Duk da gargadin da muka musu sau biyu, kamfanin bai dauki wani mataki domin magance matsalar ba.

"Yanzu kuma an sauya asibitin Dawaki zuwa cibiyar killace wadanda suka kamu da Covid-19, hakan yasa gwamnati ta rufe kamfanin."

Kwamishinan ya musanta ikirarin cewa an rufe kamfanin ne saboda dalilai na siyasa.

A bangarensa, mataimakin manajan kamfanin, Aliyu Ibrahim ya nuna rashin gamsuwarsa game da dalilin rufe kamfanin duba da cewa akwai kamfanoni irin na su 3O a jihar.

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya kuma yi ikirarin cewa kamfanin ta dakatar da ayyukan ta na mako daya domin shirye shiryen kare ma'aikatan ta daga coronavirus.

Ya ce, "Tun da muka dakatar da aiki a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, ma'aikatan mu suna hutu kuma mun kashe injinan mu."

Mr Ibrahim ya ce kamfanin za ta bi hanyoyin da doka ta tanada domin magance matsalar kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel