Ba zunubi bane mata ta kaurace wa shimfidar mijinta saboda coronavirus - Malamin addinin Musulunci

Ba zunubi bane mata ta kaurace wa shimfidar mijinta saboda coronavirus - Malamin addinin Musulunci

Wani malamin addinin musulunci a kasar Saudi Arabia ya ce halas mata su kauracewa shimfidar mazajensu wadanda ba su kiyayye ka'idojojin kare kansu daga kamuwa daga muguwar annobar coronavirus kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sheikh Abdulla al-Mutlaq, mamba na kungiyar manyan malaman addinin musulunci a kasar, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayar da wata ta aiko masa a shirin addinin da ake gudanarwa a talabijin mai suna 'Fatwa' da aka watsa wa a gidan talabijin na kasar.

Mutlaq ya ce, "Ba zunubi ki ka aikata ba kwata-kwata .. ki na kare kan ki ne."

Ba zunubi bane mata ta kaurace wa shimfidar mijinta saboda coronavirus - Malamin addinin Musulunci

Ba zunubi bane mata ta kaurace wa shimfidar mijinta saboda coronavirus - Malamin addinin Musulunci
Source: Twitter

Matar auren ta ce mijin ta baya zama a gida kuma baya kiyayye dokokin da aka saka a kasar na takaita zirga-zirga.

DUBA WANNAN: Kungiyar Al-Qaeda ta goyi bayan tsarin killace kai don kare yaduwar annobar coronavirus

Ta kara ta bayyana fargabar cewa tana iya kamuwa da kwayar cutar ta coronavirus idan ta amince su kayi kwanciya irin ta sunah.

Ya kara da cewa, "Ki yi wa kan ki rigakafi ki kaurace masa. Idan miji yana sakaci, mata ta na da ikon ta kaurace masa."

Kasar ta Saudiyya ta sanar da cewa an samu mutane 1,720 da suka kamu da kwayar cutar inda mutum 16 suka mutu kawo yanzu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito.

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar 'yan ta'addan Al-Qaeda wacce ta mayar da hankali wajen kawar da al'adun turawan yamma da gwamnatocin su, sun amincewa da tsare-tsaren Cibiyar Lafiya ta Duniya (WHO) na killace kai a matsayin hanyar yaki da cutar coronavirus a fadin duniya.

A wani jawabi ga manema labarai da kungiyar ta mika ga jaridar HumAngle a ranar Talata, Al-Qaeda ta jawo hankula ne ta hanyar amfani da hadisai wajen nuna wa al'umma abinda ya kamata a yi a yayin barkewar annoba.

Daga cikin hadisan akwai wadanda suka yi magana a kan zama a waje ba tare da bari ba matukar annoba ta barke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel