Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 1 a yau a Abuja

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 1 a yau a Abuja

Labarin da ke shigowa da daga cibiyar takaita yaduwar cuttutuka a Najeriya NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum daya da ya kamu da cutar Coronavirus a birnin tarayya, Abuja.

Mun kawo muku cewa A yau Lahadi, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa na samu karin mutane hudu masu dauke cutar coronavirus (COVID-19), yanzu adadin masu cutar a Najeriya 26.

Hukumar takaita yaduwar cututtuka (NCDC) ta sanar da hakan da safiya Lahadi a shafin raayi da sada zumuntarta na Tuwita.

Jawabin yace “Misalin karfe 08:05 am na ranar 22 ga Maris, an tabbatar da asu dauke da cutar Coronavirus 26 a Najerita. Cikinsu an sallami biyu da suka samu sauki.“

“Don sanin adadin wadanda suka kamu da cutar, ku garzaya http://covid19.ncdc.gov.ng“

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel