Rikicin APC: Uzodinma ya na ganin akwai hannun Wike a tirka-tirkar Oshiomhole

Rikicin APC: Uzodinma ya na ganin akwai hannun Wike a tirka-tirkar Oshiomhole

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya yi kira ga Takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, da ya rika tunani kafin ya tsoma baki game da abin da ya shafi harkar siyasa.

Gwamnan na Imo ya ce bai yi nadamar kalamansa ba inda ya fito ya zargi manyan PDP irinsu Nyesom Wike da hannu a rikicin da jam’iyyar APC ta samu kanta kwanaki.

Mai girma gwamnan ya jefi Nyesom Wike da hannu a yunkurin tunbuke shugaban jam’iyyar APC Kwamred Adams Oshiomhole daga kujerarsa, wanda a karshe hakan ya faskara.

An rahoto Uzodinma ya na cewa “A maimakon ya zauna ya bibiyi matsalolin jam’iyyarsa, Wike ya na ganin shiriritar da manyan batutuwan kasa za su jawo masa suna.”

Nyesom Wike ya yi hira da ‘Yan jarida, ya karyata wannan zargi na Hope Uzodinma. Wike ya yi kaca-kaca da maganganun da Uzodinma ya yi ta bakin Oguwike Nwachuku.

KU KARANTA: 'Yan daba sun kai wa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso hari a Kano

Rikicin APC: Uzodinma ya na ganin akwai hannun Wike a tirka-tirkar Oshiomhole

Uzodinma ya na ganin Wike ya bada gudumuwar tsige Oshiomhole
Source: Twitter

“Na karanta cewa Sanata Hope Uzodinma ya ce PDP sun sa hannu wajen yunkurin tsige shugaban jam’iyyar APC na kasa. Abin takaici wannan karya ce.” Inji Wike.

Wike ya soki maganganun Uzodinma, ya ce ba su da tushe kuma babu gaskiya a cikinsu. A cewarsa jam’iyyar APC ta na kokarin kawo cikas ga bangaren shari’a a Najeriya.

Gwamnan na PDP ya ba Malaman shari’a shawarar su kare kansu daga farmakin da ya ce APC mai mulki ta kawo masu, domin jam’iyyar APC ba ta nufin kasar nan da alheri.

“Uzodinma ‘Dan aiken APC ne a lokacin da ya ke PDP, shiyasa ya goyi bayan Ali Modu Sheriff, amma su ka sha kashi.” Wike ya ce babu abin da ya hada PDP da rikicin APC.

“Abin takaici ne ace wadanda akwai abin tambaya game halinsu su na rike da gwamnati.” Wike ya yi wannan magana ne a gidan gwamnatin Ribas da ke Garin Fatakwal.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel