Hafsah Gambari: Matar da aka haifa a gidan Sarki, ta auri Sarki, ta haifi Sarakuna 2 a Najeriya

Hafsah Gambari: Matar da aka haifa a gidan Sarki, ta auri Sarki, ta haifi Sarakuna 2 a Najeriya

Mahaifiyar Sarakan Kano ta zama abin labari a yanzu bayan da jama’a su ka samu labarin irin baiwar da Ubangiji ya yi mata na kashin girma da darajar sarauta.

Hafsatu Sulu Gambari, Mai dakin Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ce. Mijinta Mai martaba Ado Bayero ya shafe shekaru 50 ya na mulki a Kano tun a shekarar 1953.

Kai bari ma dai, wannan Baiwar Allah ta fito ne daga gidan sarauta ita kanta domin Mahahifinta shi ne tsohon Sarkin Ilorin mai rasuwa watau Mai martaba Sulu Gambari.

Yanzu haka bayan rasuwar Mahaifinsu,‘Danuwanta, Mai martaba Alhaji Ibrahim Sulu Gambari shi ne ya ke rike da sarautar kasar Ilorin a Jihar Kwara da ke Kudancin kasar.

Kara karanta wannan

Shahararen Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Ya Shiga TikTok, Ya Bayyana Abin Da Zai Rika Wallafawa Kullum

Shekaru fiye da 20 da su ka wuce Sanusi Lamido Sanusi wanda Jika ne wurin tsohon Sarkin Kano kuma ‘Dan Ciroma Aminu Sanusi II. ya auri ‘Diyarta Sadiya Ado Bayero.

KU KARANTA: Manyan kasar Yarbawa sun soki Ganduje a kan tsige Sanusi II

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A tsakiyar shekarar 2014, Ubangiji ya karbi ran Mai gidanta kuma Sarkin Kano Ado Bayero. Surukin na ta watau Sanusi II shi ne wanda ya gaji Mijinta a kan karaga.

Ba a samu kyakkyawar alaka tsakanin babban ‘Dan tsohon Sarki watau Sanusi Ado Bayero da Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II wanda a karshe aka tube masa rawani.

Wannan sabani ya jawo manyan ‘Ya ‘yan Hajiya Hafsat Gambari watau Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero su ka samu sarautar Wambai da Ciroman Kasar Kano.

A 2019 ne aka kirkiri sababbin Masarautu a Kano, aka nada Aminu Bayero ya zama Sarkin Bichi. A 2020 ‘Dan na ta ya zama Sarkin Kano, shi kuma Nasiru Bayero ya canjesa.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano ya Nada Sabbin Walin Kano da Sarkin Bai a Masarautarsa

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel