Sarkin Kano ya Nada Sabbin Walin Kano da Sarkin Bai a Masarautarsa

Sarkin Kano ya Nada Sabbin Walin Kano da Sarkin Bai a Masarautarsa

  • Mai martaba, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano ya nada sabbin mambobi biyu na majalisar nada sarakuna a masarautar Kano
  • Bayan nan, Alhaji Bashir Mahe Bashir shi ne Walin Kano na bakwai yayin da Mansur Mukhtar ya tabbatar sabon sarkin Bai na tara a tarihin masarautar
  • Manyan masu sarautar gargajiya, shugabannin siyasa da masu fadi a ji daga ciki da wajen jihar Kano sun shaida nadin sarautar

Kano - Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nada mutum biyu matsayin sabbin ‘yan majalisar nadi sarakun da sarautar Sarkin Bai da Walin Kano.

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano ya Nada Sabbin Walin Kano da Sarkin Bai a Masarautarsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bashir Mahe Bashir a halin yanzu shi ne Walin Kano na bakwai wanda ya gaji mahaifinsa Mahe Bashir Wali wanda yana raye amma yayi murabus daga mukaminsa saboda tsufa da rashin lafiya.

Mansur Mukhtar, tsohon ministan kudi kuma mataimakin shugaban Bankin Cigaban Musulunci yanzu shi ne Sarkin Bai na tara tun bayan jihadin Usmanu Danfodio zuwa yanzu a tarihin masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Jami’an Gwamnati 7 Da Shugaba Buhari Ya Tsige Daga Kujerunsu

Kafin rasuwarsa, mahaifinsa shi ne ‘Dan majalisar nada sarakuna da yafi dadewa na masarautar Kano tun bayan kasuwar masarautar a karni na 19.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kwashe shekaru 63 a matsayin hakimi, kansila da mai nada sarakuna kafin rasuwarsa yana da shekaru 95 a duniya.

A yayin jawabi ga Daily Trust, uwargidan sabon Sarkin Bai, Hadiza Mansur, tayi fatan Allah yayi wa maigidanta jagora.

“Yau rana ce ta tarihi a rayuwarmu. Muna fatan wannan matsayin da Allah ya kai shi, Ya bashi damar sauke nauyin tare da yi mishi jagora. Muna fatan duk wadanda suka zo taya mu murna zasu koma gidajensu lafiya.”

Nadin sarautar ya samu halartar manyan masu sarautar gargajiya, ‘yan siyasa da shugabannin al’umma daga masarautu daban-daban a ciki da wajen jihar Kano.

Bayan shekara 65 a kan gadon sarauta Sarkin Ban Kano, Adnan Mukhtar ya rasu a daren Juma'a

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Gwangwaje ‘Yan Kannywood da Kyautar N50m

A wani labari na daban, a ranar Juma’a, 3 ga watan Disamba, 2021, aka samu labarin rasuwar Sarkin Ban Kano, Mukhtar Adnan, wanda ya na cikin dattawan Arewa.

BBC Hausa ta fitar da rahoton rasuwar Alhaji Mukhtar Adnan dazu da safe. An bayyana cewa Sarkin Bai ya cika ne da tsakar dare, kafin asubar yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: