Shahararen Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Ya Shiga TikTok, Ya Fada Abin Da Zai Rika Wallafawa Kullum

Shahararen Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Ya Shiga TikTok, Ya Fada Abin Da Zai Rika Wallafawa Kullum

  • TikTok, kamfanin dandalin sada zumunta na wallafa gajerun bidiyo ya samu sabon mamba, Sanata Orji Uzor Kalu
  • Sanata Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya sanar da shigansa dandalin sada zumuntar a ranar Juma'a, 28 ga watan Oktoba
  • Babban bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bude shafin TikTok, dandalin wallafa gajerun bidiyo mallakar China

Sanata Kalu ya sanar da shigarsa TikTok a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 28 ga watan Oktoba, yana mai cewa ya yi hakan ne don karfafa zumuntar da ke tsakaninsa da abokansa da masu masa fatan alheri.

Tsohon gwamnan na Jihar Abia ya ce yana fatan zai rika wallafa bidiyon ayyukansa na siyasa da ma wanda ba na siyasa ba.

Kara karanta wannan

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

Kalu TikTok
Fitaccen Tsoshon Mai Neman Takarar Shugaban Kasa A APC Ya Shiga TikTok, Ya Fada Abinda Zai Rika Dorawa Kullum. (Photo: Senator Orji Uzor Kalu)
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan majalisar na tarayya ya bukaci abokansa kada su bari a basu labari game da abin da ke tafe.

Kalamansa:

"Domin karfafa zumuncin da ke tsakani na da ku, abokai na da masu fatan alheri, na bude shafin TikTok, ta wannan manhajar ina fatan rika wallafa bidiyon ayyukan da na ke yi a kullum na siyasa da wanda ba na siyasa ba.
"Kada ku bari a baku labari, ku bi nan @ouktiktok."

Mutanen Mazabar Sanatan Kudu Sun Juya Masa Baya Saboda Yana Goyon Bayan Tinubu Ya Zabi Abokin Takara Musulmi

Mutane daga mazabar bulaliyar majalisar tarayya kuma sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu, sun raba jiha da shi, saboda ya shawarci dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya zabi musulmi a matsayin abokin takararsa a 2023, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ba Wa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

Kalu, wanda ya jadada cewa babu matsala idan musulmi da musulmi sun yi takara, ya ce kuskure ne Tinubu, wanda musulmi ne cikin marasa rinjaye a kudu ya zabi kirista daga arewa wanda shima yana cikin marasa rinjaye a matsayin mataimakinsa.

A martaninsa, Basaraken garin Abiriba, Eze Kalu Kalu Ogbu (Enachoken) ya ce abin da tsohon gwamnan ya fada ba su gamsu da shi ba kuma bai bada ma'ana ba.

2023: Kalu ya bayyana matsayinsa na karshe kan shugabancin kasar Igbo, ya aika sako ga yan kudu

Kalu ya ce zai yi wahala ga wani Ibo ya ci shugaban kasa ba tare da an bawa yankin damar fitar da dan takara su kadai ba.

Don haka, ya yi kira ga yan siyasa daga yankinsa da suke son kujerar su yi hakuri har lokacin da manyan jam'iyyu za su basu damar fitar da yan takara

Asali: Legit.ng

Online view pixel