Tsige Oshiomole: Yan sanda sun kulle hedkwatar jam'iyyar APC

Tsige Oshiomole: Yan sanda sun kulle hedkwatar jam'iyyar APC

Sakamakon dakatad da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa, Adams Oshiomole, a ranar Laraba da kotu tayi, hukumar yan sanda ta garkame hedkwatan jam'iyyar dake Blantyre Street, unguwar Wuse 2, Abuja.

Da safiyar yau Alhamis, jami'an yan sanda akalla hamsin sun yiwa hedkwatar da titin gaba daya zobe.

A cewar majiya mai sika, kwamishanan yan sandan birnin tarayya da mataimakansa guda biyu sun dira ofishin da safen nan.

Majiyar ta ce an tura jami'an yan sanda hedkwatar ne saboda labarin da aka samu cewa dakataccen shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomole, na shirin zuwa ofishin.

Wani jami'in tsaro a hedkwatar APC ya bayyanaw manema labarai cewa yan sandan na samun labarin cewa Oshiomole na shirin zuwa aka turo jami'ai da yawa.

Ya ce kwamishanan yan sandan ya bada umurnin cewa kada a sake a bari kowa ya shiga cikin sakatariyan har sai wani mamban kwamitin gudanarwa jam'iyyar ya zo wajen.

An hana dukkan ma'aikatan hedkwatar da suka zo aiki shiga.

Ku dakaci karin bayani anjima.....,

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel