Abun bakin ciki: Yan gida daya su 3 sun mutu a gobara

Abun bakin ciki: Yan gida daya su 3 sun mutu a gobara

- Wata gobara da ta afku a baya-bayan nan ta yi sanadiyar mutuwar yan gida daya su uku a jahar Anambra

- Wadanda suka mutun sun kasance mata biyu da namiji daya yan tsakanin watanni biyu zuwa shekara 5

- An tattaro cewa gobarar ta kama ne a gidan Chukwuma Aduhuba a ranar 15 ga watan Fabrairu

Wasu yan uwan juna su uku sun babbake har lahira a ranar Asabar a gidansu da ke kauyen Chelekwe, Okija a karamar hukumar Ihiala da ke jahar Anambra.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa har yanzu ba a san abun da ya haddasa gobarar ba.

Abun bakin ciki: Yan gida daya su 3 sun mutu a gobara
Abun bakin ciki: Yan gida daya su 3 sun mutu a gobara
Asali: UGC

Da ya ke tabbatar da lamarin, a Wani jawabi daga jami’in hulda da jama’a a Anambra, SP Haruna Mohammed, ya ce da misalin karfe 2:00 na tsakar dare, an yi gobara a gidan wani Chukwuma Aduhuba na kauyen Ugwu Chelekwu, a Okija na karamar hukumar Ihiala da ke jahar Anambra.

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: An yi garkuwa da babban jami'in gwamnatin Nasarawa

Sakamakon haka yaransa uku masu suna Chimankpan Aduhuba dan shekara 5, Munachimso Aduhuba mai shekara 2 da Kamsiyochi Aduhuba mai watanni 2 sun babbake sannan suka mutu a nan take yayinda kayayyakin miliyoyin naira suka kone.

A wani labarin kuma, mun ji cewa mutane ashirin da biyu, yawancinsu mata da kananan yara, sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Kafur da ke kan hanyar Kankia zuwa Danja a jihar Katsina.

Mummunan hatsarin , wanda ya faru ranar Asabar, ya ritsa da wasu motoci kirar J5 guda biyu wadanda suka yi karo. Motocin biyu na dauke da jimillar mutane 36.

Kakakin hukumar kiyaye hatsari ta kasa (FRSC) a jihar Katsina, Abubabakar Usman, ya shaida wa gidan talabijin na Channel ce wa mutane 11 sun samu rauni sakamakon hatsarin, yayin da mutane uku suka tsira babu ko kwarzane.

Motocin biyu da hatsarin ya ritsa da su, sun kama wuta nan take bayan sun yi karo da juna, lamarin da ya yi sanadiyyar konewar fasinjoji 22.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel