Matar aure ta fadi wanwar bayan mijinta ya nausheta a wajen da aka yi mata tiyatar haihuwa

Matar aure ta fadi wanwar bayan mijinta ya nausheta a wajen da aka yi mata tiyatar haihuwa

- Wani magidanci a jihar Enugu ya samu kiran gaggawa daga hukumar 'yan sanda a kan zargin cin zarafin matar shi

- An zargi magidancin da yi wa matar shi dukan kawo wuka wanda yayi sanadiyyar faduwarta rai a hannun Allah

- Bayan sabanin da ya shiga tsakaninsu, yayi mata mugun duka tare da dukan ta a wajen da aka yi mata aiki don cire da daga cikin ta a asibiti

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, hukumar 'yan sandan jihar Enugu ta yi wa wani miji kiran gaggawa bayan wata wallafa a kan shi da wani yayi.

Wani bawan Allah ya bukaci taimakon jama'a a shafin tuwita don neman mafita ga wata matar aure da mijinta yayi mata dukan kawo wuka.

Ba dukan bane sabon abu, don an saba cin zarafin mata ko ma'aurata a Najeriya. Dukan da yayi wa matar ne a wajen dinkin aikin da aka yi mata na cire da daga cikinta.

Bayan 'yar hatsaniyar da ta wanzu tsakanin ma'auratan, mijin ya kama matar inda ya lakada mata dukan kawo wuka tare da dukan wajen da aka yi mata aiki don cire da. Wannan lamarin kuwa yasa ta fadi rai a hannun Allah.

Wani mutum da ya ga abinda ya faru, sai ya wallafa labarin a shafin shi na tuwita tare da rokar taimakon jama'a har wallafar shi ta kai ga hukumomin da ke da alhakin daukarwa matar fansa.

KU KARANTA: Biyu babu: 'Yan Najeriya da aka yiwa karyar za a kai su Turai sun tsinci kansu a kasar Ghana

Babu dadewa kuwa wani mutum yayi kira ga hukumar 'yan sanda ta hanyar jawo hankalinsu a kan wannan wallafar.

Babu dadewa hukumar tayi wa wannan mai gida madakin matarshi kiran gaggawa.

Idan ba zamu manta ba, a makon da ya gabata ne Legit.ng ta ruwaito yadda wani saurayi a jihar Bauchi mai suna Solomon ya kashe budurwarshi ta hanyar soka mata wuka a bayanta.

Kamar yadda budurwar ta bayyana kafin ta ce ga garinku, Solomon yayi hakan ne saboda tsananin bakin kishi. Budurwar ta amsa wayar wani ne a gaban saurayin nata, lamarin da ya tashi bakin kishin shi har ya kai ga soka mata wuka wacce tayi ajalinta bayan wuni daya da tayi tana zubar da jini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel