Yanzu Yanzu: Buratai ya sake bude hanyar Maiduguri-Damboa bayan watanni 13 a rufe

Yanzu Yanzu: Buratai ya sake bude hanyar Maiduguri-Damboa bayan watanni 13 a rufe

- Laftanal Janar Tukur Buratai, shugaban hafsan soji a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, ya sake bude babban hanyar Maiduguri-Damboa bayan rundunar soji ta rufe shi saboda rashin tsaro

- Buratai ya ba matafiya da yan farin hula da ke bin hanyar tabbacin samun cikakken tsaro, cewa ya umurci dukkanin kwamandoji da su samar a tsaro ga dukkanin masu bin hanyar

- Hakan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya roki da a sake bude manyan titunan

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, ya sake bude babban hanyar Maiduguri-Damboa bayan rundunar soji ta rufe shi saboda rashin tsaro.

Buratai ya bayyana a lokacin bikin sake bude hanyar wanda aka gudanar a tashar bincike na Molai, wajen birnin Maiduguri cewa, a yanzu an bude babban hanyar ga masu motoci da masu tafiya a kafa da ke zirga-zirga tsakanin Maiduguri zuwa Biu da sauran garuruwa.

Yanzu Yanzu: Buratai ya sake bude hanyar Maiduguri-Damboa bayan watanni 13 a rufe
Yanzu Yanzu: Buratai ya sake bude hanyar Maiduguri-Damboa bayan watanni 13 a rufe
Asali: Depositphotos

Shugaban sojin ya ba matafiya da yan farin hula da ke bin hanyar tabbacin samun cikakken tsaro, cewa ya umurci dukkanin kwamandoji da su samar a tsaro ga dukkanin masu bin hanyar.

Idan za a tuna, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi roko kan sake bude manyan tituna. Ya yi rokon ne a lokacin da ya ziyarci ministan tsaro, Basir Magashi.

KU KARANTA KUMA: Muna kokarin kawo jituwa tsakanin Ganduje da Sarkin Kano — Ibrahim Shekarau

A halin da ake ciki, mun ji cewa babbar jam’iyyar PDP ta bayyana gamsuwarta da kamun ludayin gwamnan jahar Borno na jam’iyyar APC, Farfesa Babagana Umara Zulum sakamakon yadda yake tafiyar da harkar tsaro a jahar, tare da sauran ayyuka.

Shugaban sashin jam’iyyar PDP, Usman Badeiri ne ya bayyana haka ne inda yace Gwamna Zulum ya basu mamaki duba da manyan ayyukan da yake gudanarwa a jahar Borno, duk kuwa da cewa dan jam’iyyar APC ne.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban jam’iyyar, Usman Badeiri ya jaddada cigaba da zama a cikin jam’iyyar PDP daram dam dam, ba ma shi kadai ba, hatta shuwagabannin jam’iyyar a matakin jaha, kananan hukumomi da mazabu ba zasu fita daga cikinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng