PDP: Tambuwal ya canji Dickson a matsayin Shugaban Gwamnoni

PDP: Tambuwal ya canji Dickson a matsayin Shugaban Gwamnoni

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP kamar yadda mu ke samun labari.

Wani daga cikin Masu ba gwamnan shawara, Mohammad Bello, shi ne ya sanar da Manema labarai wannan a wani jawabi da ya fitar ba da dadewa ba.

Malam Mohammed Bello ya tabbatar da zama gaskiyan rade-radin da aka dade ana yi cewa Aminu Waziri Tambuwal ne zai gaji kujerar Mista Seriake Dickson.

An cin ma wannan matsaya ne a wani taro da gwamnonin jam’iyyar PDP su ka halarta na zaman majalisar NEC na 88 da aka gudanar a Birnin Tarayya Abuja.

Gwamna Seriake Dickson wanda bai halarci wannan taro da aka yi a Garin Abuja ba, zai bar kan karagar mulki ne a Ranar Litinin 3 ga Watan Fubrairun 2020.

Da yake jawabi bayan an daura masa wannan nauyi a kai, Rt. Hon. Aminu Tambuwal ya sha alwashin ciyar da jam’iyyar hamayyar gaba a wa’adin da zai yi.

KU KARANTA: Ana tsere zama Shugaban Gwamnonin PDP tsakanin Gwamnonin 3

PDP: Tambuwal ya canji Dickson a matsayin Shugaban Gwamnoni
Gwamna Tambuwal ya zama Shugaban Gwamnonin PDP
Asali: UGC

Gwamnan na Sokoto ya bayyana cewa zai tafi da kowa a karkashinsa. Mafi yawan kusoshin da su ke Wadata Plaza ne su ka yi wa gwamnan mubaya’a dazu.

Mista Seriake Dickson ya karbi wannan kujera ne daga hannun tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, wanda ya sauka daga kan mulki a 2018.

A baya tsofaffin gwamnoni jam’iyyar; Godswill Akpabio da kuma Olusegun Mimiko sun rike wannan mukami. A 2013 ne gwamnonin PDP su ka kafa kungiyar.

Kawo yanzu babu wanda ya san abin da ya hana shugaban da ya bar gado, Mr. Dickson halartar wannan taro da ya kamata ace ya mika kambun mulki ga Magajinsa.

Yanzu haka Aminu Tambuwal shi ne mataimakin shugaban gwamnonin Najeriya a karkashin lamar kungiyar NGF wanda Dr. Kayode Fayemi ya ke jagoranta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel