Alkali ya samu Darektan Janar na NCAC da laifin raina maganar kotu

Alkali ya samu Darektan Janar na NCAC da laifin raina maganar kotu

Babban kotun tarayya da ke zama a Maitama a Garin Abuja, ya yankewa Darekta Janar na hukumar NCAC hukuncin dauri.

Wani Alkalin babban kotun da ke birnin tarayya Abuja ya samu shugaban wannan hukuma da laifin wargi da raina hankalin kotu.

Alkali mai shari’a Jude Okeke shi ne ya bada wannan hukunci da nufin cewa zai zama darasi ga sauran masu sabawa umarnin kotu.

Rashin bin umarnin kotu da maganar Alkali babban laifi da da ke nuna mutum ya na ganin cewa kuliya ba ta isa ba inji Jude Okeke.

Alkali Jude Okeke ya bada umarni a rufe Mista Otunba Olusegun Runsewe a gidan yarin da ke Garin Kuje domin ya koyi darasi.

KU KARANTA: Okorocha ya wawuri biliyoyi a lokacin ya na Gwamna - Bincike

Alkali ya samu Darektan Janar na NCAC da laifin raina maganar kotu
Darekta na Janar na NCAN zai yi zaman gidan yari a Najeriya
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Alkalin ya ce za a tsare shugaban hukumar NCAC har sai lokacin da ya rabu da halin na sa.

Haka zalika Alkali ya nemi shugaban ‘Yan sandan Najeriya ya sanar da kotu game da cika wannan umarni da aka ba jami’an tsaro.

An yanke wannan hukunci ne sakamakon karar da kamfanin Ummakalif ya shigar da Darekta Janar na hukumar da ke kula da al’adu.

Sauran wadanda aka hada a cikin karar sun hada da Ministan yada labarai da al’adu da kuma hukumar FCDA, da kuma Ministan Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel