Fasto ya kashe kansa da matarsa a gaban masu bauta a cocinsa

Fasto ya kashe kansa da matarsa a gaban masu bauta a cocinsa

Wani fasto a kasar Kenya ya matukar girgiza mabiyansa, bayan ya kashe matarsa kafin daga bisani ya kashe kansa duk a gabansu, yayin da suka halarci Cocinsa domin gudanar da bautar ranar Lahadi.

A cewar kafafen yada labarai na cikin gida, limamin Cocin mai suna Elijah Misiko ya bar wurin zamansa tare da nufar wajen zaman matarsa, Ann Mughoi, wacce ita ma fasto ce a cocin.

A nan ne ya fito da wukar da ya boye a cikin ambulan kuma ya soke ta. Da wannan wukar ya kara amfani wajen kashe kansa, lamarin da yayi matukar girgiza masu bautar.

“Ya yi tattaki har zuwa inda matarsa take a cocin kamar zai sanar mata da wani abu daban,” Kamar yadda kwamandan ‘yan sandan Mombasa, Julius Kiragu ya sanar.

“Daga nan ne ya dau wukar da ya booye cikin ambulan ya soketa har sau biyu. A tunaninsa ta mutu. Daga nan sai ya soki kansa har sau uku a ciki tare da yanke makogwaronsa.”

Misiko ya mutu a take sakamakon raunin da yaji amma Mughoi ta mutu ne a wani asibiti bayan sa’o’i kalilan, cewar ‘yan sandan.

DUBA WANNAN: Ba mu yi karin kudin wutar lantarki ba - FG

Ma’auratan sun kasance suna samun rashin jituwa akai-akai a kan shugabanci tare da sahihin mamallakin cocin, Julius Kiragu ya sanar da CNN.

A 2017, an garkame Misiko a Mombasa bayan da matarsa ta zargesa da yunkurin kashe ta. Washegarin ranar da aka garkamesa ne kuwa aka sake shi bayan da ‘yan sandan suka gano babu kamshin gaskiya a wannan zancen.

Mahaifan ‘ya’ya hudun basu zama tare tun kusan shekaru biyu da suka gabata sakamakon fadan nasu da yaki ci, yaki cinyewa.

A wasiyyar karshe da Misiko ya rubuta mai yawan shafuka har 17, ya zargi Mughoi da sauya mamallakin cocin, wanda yace tare suka kafa shi amma ta mayar da sunanta ita kadai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel