Allah Sarki: Wata mata mai tsohon ciki ta mutu bayan maciji ya sare ta a cikin bandaki a Kaduna

Allah Sarki: Wata mata mai tsohon ciki ta mutu bayan maciji ya sare ta a cikin bandaki a Kaduna

- Wata mata dauke da cikin watanni takwas tayi bankwana da duniya bayan maciji ya sareta

- Macijin ya sareta ne a bayi bayan da ta tsuguna zatayi alwalar sallar asuba a ranar Alhamis

- Asibitocin da aka garzaya duk sun ce basu da maganin dafin bayan kalubalen rashin titi mai kyau da aka fuskanta

Wata mata dauke da tsohon ciki na watanni takwas tayi bankwana da duniya sakamakon cizon maciji. Lamarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Janairu 2020, a garin Kaduna bayan da maciji ya sareta.

Kanin mijinta mai suna ZunNoorayne ne ya wallafa labarin a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita, da yammacin ranar Alhamis din.

Kamar yadda ya wallafa, marigayiyar ta je zagayawa bayi ne a sa'o'in farko na ranar Alhamis. Amma kuma a rashin sani, macijin na cikin matsugunin. Macijin ya sareta amma bata sani ba, don kuwa ta cigaba har tayi alwala tare da yin sallar asuba. Amma abun haushin da tashin hankali shine yadda asibitoci suka kasa yin komai a kai.

KU KARANTA: Tirkashi: Mata ta sayar da mijinta sukutum akan N6,000, ta siyawa 'ya'yanta kayan sawa

Kamar yadda ya wallafa, "A yau ne matar yayana mai dauke da cikin wata takwas ta riga mu gidan gaskiya. Maciji ne ya sareta a sa'o'in farko na ranar Alhamis amma bata sani ba. Tayi alwala kuma tayi sallah, daga bisani ta fara jin ciwon.

"A take aka garzaya da ita asibiti bayan an fahimci abinda ya faru. Tashin hankali na farko shine yadda titi babu kyau. Sai kuma asibitoci da suka ce basu ajiye maganin dafi. A asibitin NNPC tace ga garinku."

ZunNoorayne ya bayyana cewa, ta rasu ta bar mijinta da yaronta mai shekaru biyu a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel