Budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya dirkawa kawarta ciki kwana hudu da zuwanta gidansu

Budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya dirkawa kawarta ciki kwana hudu da zuwanta gidansu

- Wata budurwa ta wallafa yadda saurayinta yayi nasarar dirkawa kawarta ciki a cikin kwanaki hudu tak

- Tayi bayanin cewa, da kanta ta ba kawar matsuguni a gidan saurayinta saboda tana neman wajen zama

- Tuni saurayin ya amsa laifinshi tare da dora laifin a kan budurwarshi don ita ta kawo mishi mata har gida

Wani saurayi ya dirkawa kawar budurwarshi ciki a cikin kwanaki hudu da ya basu masauki.

Budurwar dai ta taimakawa kawarta ne da wajen zama bayan da kawar ta roketa. Ta amince mata da tazo su zauna tare da saurayinta ne.

Kamar yadda budurwar ta bayyana cikin tashin hankali, ta gano kawarta na dauke da juna biyu ne bayan kwanaki hudu da ta tare dasu kuma saurayinta ne yake da cikin.

KU KARANTA: Daga gwada mijina da aminiyata, yanzu gashi nan yana shirin auro mini ita - Mata ta koka

Kamar yadda ta rubuta, "Kawata na neman matsuguni ne ni kuwa na tausaya. A matsayina na kawa ta gari, sai nace tazo ta zauna tare da saurayina tunda nima a nan nake zama. Tuni dai ta samu ciki kuma nashi ne don ya amsa. Dalilinshi shi ne don ni na kawota. Naji dadi da hakan ta faru kuma duk a cikin kwanaki hudu kacal. Da na aureshi, da kuwa na shiga uku."

Budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya dirkawa kawarta ciki kwana hudu da zuwanta gidansu

Budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya dirkawa kawarta ciki kwana hudu da zuwanta gidansu
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel