DPR ta rufe gidajen mai 10 a Kaduna

DPR ta rufe gidajen mai 10 a Kaduna

Sashin kula da labarkatun man fetur na DPR ya rufe gidajen mai 10 da na iskar gas guda 4 a jihar Kaduna sakamakon laifuka daban-daban.

Shugaban DPR ba yankin Arewa maso yamma, Isa Tafida ya sanar da manema labarai hakan yayin wani aikin duba wauraren da aka kulle din.

Ya tabbatar da cewa suna da alifukan da suka kunshi rashin zuba man fetur ga kwastomomi na kudinsy, waskar da kayan man fetur din, aiki babu lasisi da kuma rashin kula da dokokin kariya.

DUBA WANNAN: Sanata Abaribe ya bukaci Buhari ya saki El-Zakzaky

Sauran laifukan sun hada da rashin bin dokokin kafuwar gidan man, ginin da kuma rashin lasisin DPR din ko kuma saka injin ba tare da amincewar hukumar ba.

Tafida ya bayyana cewa cibiyar ta duba a kalla gidan mai 768 da kuma wajen iskar gas 38 a cikin watanni uku na karshen shekarar 2019.

Yayi bayanin cewa, amfanin hakan kuwa shine tabbatar da cewa sun bi doka kuma ba a dakile ‘yan kasuwar ba ballantana cikin lokacin wannan bikin na Kirsimeti da sabuwar shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel