Yanzu-yanzu: EFCC ta damke Shehu Sani kan zargin damfarar N7m

Yanzu-yanzu: EFCC ta damke Shehu Sani kan zargin damfarar N7m

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta damke Shehu Sani, Sanatan da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019. The Nation ta ruwaito.

A cewar majiyar, an damke Shehu Sani ne kan zargin karban $20,000 daga hannun mai kamfanin motocin ASD.

Majiyar tace: "An ce ya karbi $20,000 daga hannun mai kamfanin ASD da sunan cewa shi abokin shugaban EFCC."

"Bayan an damkeshi, ya mayar da kudin kuma an bashi beli."

"An bukaci ganinsa amma ya ba'a sameshi ba. Da alamun ya dade yana damfarar mutane da sunan shugaban EFCC."

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel