Satar kwan fitila: Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin kwanaki 21 a gidan yari

Satar kwan fitila: Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin kwanaki 21 a gidan yari

Wani dan Najeriya mai suna Saidu Ahmadu ya samu hukuncin makonni uku a gidan maza, daga kotun Karmo mai daraja ta daya da ke babban birnin tarayya. An yanke masa wannan hukuncin ne bayan da aka kama shi da laifin ballewa tare da shiga gidan mutane. Bayan haka kuma ya saci kwan fitila.

Jaridar Within Nigeria ta gano cewa, mai shari'a Alhaji Inuwa Maiwada ya yankewa Ahmadu hukuncin makonni ukun a gidan maza ne ba tare da tara ba. Hakan ya biyo bayan balle gidan mutane tare da sata da aka kamashi da laifin aikatawa.

Wanda aka garkame din mazaunin titin Legas ne dake Gwagwa a Abuja.

DUBA WANNAN: Kotu ta daure malamin jami'a a Kano saboda kunduma ashariya

Mai karar Umar Shuaibu na Idu dake zama a fadar sarkin Karmo da ke Abuja, ya kai rahoton ne ga ofishin 'yan sanda na Utako da ke birnin tarayya a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Ukagha ya sanar da kotun cewa, wanda ake zargin da wasu mutane sun balle gidan mai karar, inda suka sace masa wasu abubuwa har da kwan fitila.

Lauyan ya kara da cewa, a yayin binciken da 'yan sanda suka gudanar, an gano cewa wanda ake zargin ya saba satar kayan mutane a yankin Karmo din.

Laifukansa kuwa sun ci karo da sashi na 76, 245 da 288 na dokokin Penal Code.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel