Rikicin fadar shugaban kasa: 'Yan garinsu Buhari sun yi wa Aisha kaca-kaca

Rikicin fadar shugaban kasa: 'Yan garinsu Buhari sun yi wa Aisha kaca-kaca

'Yan garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari sun caccaki matarsa, Aisha, kan kalaman da ta yi a ranar Laraba inda ta soki hadimin shugaban kasar na musamman, Garba Shehu.

A hirar da su kayi lokuta daban da wakilin jaridar The Punch a yammacin ranar Laraba, 'yan uwan shugaban kasar sun caccaki Aisha Buhari kan katsalandan kan abinda suka kira fallasawa duniya harkokin cikin gida.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, Aisha Buhari ta ce "Garba Shehu ne ya ce gwamnati za ta dakatar da ofishin first lady. Amma daga baya ya fadawa daya daga cikin hadimai na cewa Mamman Daura ne ya bayar da umurnin ba shugaban kasa ba. Hakan ya bakantawa matan Najeriya rai. Bai san cewa ofishin First Lady al'adda ce da ta zama doka."

Da suke tsokaci kan kalaman na Aisha Buhari, mazauna Daura, mahaifar shugaban kasa sun ce kamata ya yi Aisha ta tattauna batun da mijinta.

DUBA WANNAN: Tirkashi: Matashi mai shekaru 19 dirka wa mahaifiyarsa cikin shege

Sukar Shehu kamar sukar Buhari ne - Kungiyoyin Daura

Shugaban gamayyar kungiyoyin Daura, Mallam Muhammed Saleh a hirar da ya yi da majaiyar Legit.ng ya ce rashin jituwa tsakanin Shehu da Aisha harka ce ta cikin gida.

Ya ce kalaman da matar shugaban kasar da ya yi bai dace ba domin sukar Shehu kamar sukar Buhari ne.

Saleh ya bayar da shawarar cewa a sulhunta ayi sulhu a cikin gida.

Aisha tana bata sunan mijinta - Dattijo a Daura

Wani dattijo a Daura, Alhaji Usman Kalgi ya ce maganar da matar shugaban kasar ta yi a fili kan Shehu cin fuska ne ga Buhari.

Kalgo ya ce, Idan Aisha ta lura da wani gazawa a bangaren Shehu abinda ya dace ta yi shine ta yi wa mijinta magana amma ba ta fito bainar jama'a da batun ba.

Ya ce shugaban kasan ya tabbatar Shehu ya cancanta kafin ya nada shi mukamin.

Wani lauya mazaunin Daura mai suna Ado Lalu ya ce fito da maganan fili da Aisha ta yi ba zai warware matsalar ba.

Shima ya ce irin wannan matsalar kamata ya yi a warare ta a cikin gida.

Wannan harka ce ta cikin gida - Masarautar Daura

Mai magana da yawun masarautar Daura, Mallam Usman Ibrahim da aka yi hira d ashi a wayan tarho ya ce, " wannan harka ce ta cikin gida kuma ba mu magana a kan irin wannan harkokin."

Harka ce ta gida - Masarautar Daura

A jihar Zamfara, Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello ya shaidawa majiyar Legit.ng ta bakin hadiminsa, Alhaji Abdulkadir Usman cewa batun na gida ne.

Ya ce, "wannan batu ne na cikin gida; bai shafi aiki ba saboda haka ba za mu ce komi a kai ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel