Assha: Yadda 'bam' ta yi kaca-kaca da hannun wani dalibin sakandare

Assha: Yadda 'bam' ta yi kaca-kaca da hannun wani dalibin sakandare

Wani abu mai fashewa da ake zargin bam ne ya tashi kuma ya tsinke hannun wani dalibi da ke makarantar Glory Land dake kauyen Azugwu a jihar Ebonyi, a ranar Alhamis.

Dalibin mai suna Chibuike na aji na biyar ne a makarantar.

Lamarin ya faru ne a lokacin tara, kamar yadda majiya daga makarantar ta sanar.

Baya da dalibin da hannunsa ya fita, majiyar ta ce akwai dalibai masu yawa da suka samu rauni daban-daban.

Lamarin ya faru ne wajen karfe 11 na safiyar Alhamis, kuma ya kawo tashin hankula a makarantar da makwaftanta, in ji wata majiya.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sanatoci da ministoci da kotu ta ce su dawo da fanshon da suka karba a matsayin tsaffin gwamnoni

Wakilin jaridar Punch yace, Chibuike na ta kuka tare da wayyo a yayin da yake cikin mini. Tuni dai aka kwashesa zuwa cibiyar gaggawa da asibitin jami'ar koyarwa ta tarayya da ke Abakaliki.

Sauran daliban da suka raunata kuma suna samun kulawar masana kiwon lafiya a wasu asibitocin da ba a bayyana ba a jihar, in ji majiyar.

A lokacin da aka tuntubi kakakin hukumar 'yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta kara da cewa, basu samu rahoto ba da aka kawo wa ofishin 'yan sandan da ke Eke-Aba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel