Borno: Zulum ya kori Shugaban Ma’aikata, ya nada Kwamitin karin albashi

Borno: Zulum ya kori Shugaban Ma’aikata, ya nada Kwamitin karin albashi

Babagana Umara Zulum ya sallami shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Borno, Mohammed Hassan daga aiki. Gwamnan ya sanar da wannan ne ta bakin Sakataren gwamnatin jihar dazu.

SSG Alhaji Usman Shuwa, shi ne ya bada wannan sanarwa a wani jawabi da ya fitar yau Ranar Talata, 26 ga Watan Nuwamban 2019. Gwamnan ya nada Simon Malgwi a matsayin sabon HoS.

Jawabin ya ce: “Gwamna Babagana Zulum ya sallami Mohammed Hassan daga kujerar HOS. Ya amince da nadin Barista Simon Malgwi a matsayin sabon HOS ba tare da wani bata lokaci ba.”

Mista Simon Malgwi zai maye gurbin Mohammed Hassan. Shuwa ya ce kafin wannan nadi, Malgwi ya kasance babban Lauya kuma Sakataren din-din-din a ma’aikatar ilmi na jihar Borno.

Haka zalika Mai girma gwamnan ya kafa kwamitin da zai duba sha’anin daidaita karin albashin ma’aikata a jihar. Kwamishinan shari’an Borno, Kaka Shehu zai shugabanci wannan kwamiti.

KU KARANTA: Gwamna ya sake tona asirin tsohon Gwamna Yari a rikin Zamfara

Inuwa Yusuf, wanda shi ne shugaban kungiyar nan ta MHWUN ta ma’aikatan lafiya, zai jagoranci bangaren ‘yan kwadago na kwamitin da zai duba yadda za a karawa ma’aikatan jihar albashi.

Sabon HOS da aka nada ne zai zama shugaba na biyu na wannan muhimmin kwamiti. Zai yi aiki da Kwamishinonin kudi da kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, da tsohon Jami'i Ibrahim Jalo.

Har ila yau, Sakataren din-din-din na ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ya na cikin kwamitin tare da babban mai binciken kudi. Wani babban Sakataren jihar zai zama Magatakardan kwamitin.

Bangaren ma’aikata zai kunshi mutane 10 da aka zakulo daga kungiyoyin kwadago da ma’aikatu daban-daban da ke jihar. Kwamitin zai karkare aikinsa cikin makonni uku inji SSG Shuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel